Kamfanin wutar lantarki na kasa (TCN) ya sanar da samun gagarumin ci gaba wajen maido da layin wutar lantarki na kasa sakamakon katsewar wutar a ranar Litinin, 14 ga watan Oktoba da misalin karfe 6:48 na yamma.
“Nan take ba a yi kasa a gwiwa ba aka tsunduma aikin maido da wutar lantarki, inda tashar wutar lantarki ta Azura ta taka muhimmiyar rawa wajen maido da lantarki na wucin gadi.
- Yadda Ake Kula Da Jama’a Ya Fi Muhimmanci
- Gwamnatin Kano Za Ta Gyara Cibiyar Fasaha Da Aka Lalata Lokacin Zanga-Zanga
“Duk da ci gaban da aka samu wajen maido da wutar, da misalin karfe 10:24 na safiyar ranar Talata, TCN ta ci karo da wani dan karamin koma baya.
“Sai dai an samu nasarar maido da wutar lantarki a wurare masu mahimmanci, da suka hada da yankin Abuja da sauran manyan cibiyoyin rarraba wutar lantarki a fadin kasar.
“Katsewar wutar, bata shafi tashar Ibom ba, inda ta ci gaba da samar da wuta ga yankunan Kudu-maso-Kudu, da suka hada da Eket, Ekim, Uyo, da tashar wutar ta Itu mai nauyin 132kV.” In ji TCN