Shugaban kasa Bola Tinubu ya sanar da rasuwar, Babban Hafsan Sojin Kasan Nijeriya, Laftanar Janar Taoreed Abiodun Lagbaja, wanda ya rasu yana da shekara 56.
Sanarwar da ta fito ne daga fadar shugaban kasa, wadda Bayo Onanuga ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa Lagbaja ya rasu a daren ranar Talata a Legas bayan fama da rashin lafiya.
Shugaba Tinubu ya nada shi matsayin Babban Hafsan Sojin Kasa a ranar 19 ga Yunin 2023.
Ya fara aikin soja a makarantar horas da sojoji ta kasa (NDA), a shekarar 1987, kuma an nada a matsayin Laftanar na biyu a rundunar Infantry ta Nijeriya a ranar 19 ga Satumban 1992, a matsayin wani daga cikin wadanda suka kammala Kwas na 39.
A tsawon aikinsa, Laftanar-Janar Lagbaja ya nuna kwarewa wajen shugabanci.
Ya yi aiki a matsayin mai kula da rukunin sojoji a bataliya ta 93 da kuma 72 ta Special Forces Battalion.
Ya taka muhimmiyar rawa a wasu ayyukan tsaro a cikin gida, kamar Operation ZAKI a Jihar Binuwai, Lafiya Dole a Borno, Udoka a Kudu Maso Gabashin Nijeriya, da kuma Operation Forest Sanity a Jihohin Kaduna da Neja.
Lagbaja ya yi karatu a makarantar U.S. Army War College kuma ya samu digirin digirgir a fannin Nazarin Tsare-tsare, wanda ya nuna himmarsa wajen kwarewa da shugabanci.
Ya rasu ya bar mata, Mariya, da ‘ya’ya biyu. “Shugaba Tinubu ya mika ta’aziyyarsa ga iyalansa da rundunar sojin Nijeriya. Ya yi addu’ar Allah Ya jikansa da rahama,” in ji Onanuga.