Ana fargabar wasu leburori uku da suke aikin hakar kasa a yammacin ranar Lahadin sun mutu bayan da wata kasa ta afko kansu a wani kauye da ake kira Unguwan Ayaba da ke karamar hukumar Keffi a jihar Nasarawa.
Ma’aikatan suna ta tono jar kasa tare da loda ta a cikin wata motar dakon kasa a wurin da suke hako kasar, sai kwatsam kasar ta yanko ta afka musu ta binne mutum hudu daga cikinsu.
- Rikici Ya Ɓarke Bayan Kotun Ƙoli Ta Tabbatar Da Sule A Gwamnan Nasarawa
- Kotun Ƙolin Nijeriya Ta Tabbatar Da Zaɓen Sule A Matsayin Gwamnan Nasarawa
An ce daya daga cikinsu an yi sa a ya tsallake rijiya da baya domin ya samu ya tsira daga karkashin kasar da ta danne su, sai dai ya samu raunuka yayin da sauran mutum ukun har yanzu ake kan tono ba a gansu ba.
Masu aikin ceto mutanen da mazauna kauyukan da suka hada da ‘yan uwan wadanda abin ya shafa sun killace wurin domin tono gawarwakin ma’aikatan uku, sun fara aikin tonon tun da yammacin ranar Lahadi lokacin da abun ya faru, amma abin ya ci tura har zuwa lokacin kawo wannan rahoton.
Daya daga cikin masu aikin sa kai a wurin, Saliu Abdullahi, ya ce sun shafe fiye da sa’o’i biyu suna aikin tono ma’aikatan, ya kara da cewa ba za su bar wurin ba har sai sun hako gawarwakin ma’aikatan uku.
Shima mataimakin shugaban kungiyar masu Tipper da ke karamar hukumar Keffi, Aminu Sunusi, ya ce sun aika da injin tona domin a samu a gaggauta aikin ceto mutanen.
Sunusi ya kara da cewa za su dauki kwararan matakai don kaucewa irin matsalar da ake ciki da dakile afkuwar irin wannan hadari a nan gaba.