Ministan wajen Argentina Santiago Cafiero ya bayyana a ranar 2 ga wata cewa, bangaren Argentina ya sanar da bangaren Ingila a hukumance yayin taron ministocin harkokin wajen G20 cewa, ta yanke shawarar kawo karshen “yarjejeniyar Fradori-Duncan” da kasashen biyu suka sanya hannu game da rikicin tsibiran Falkland a shekarar 2016.
Ban da wannan, ya kuma shawarci Birtaniya cewa,ya kamata a sake fara tattaunawa kan ikon mallakar tsibiran Falkland kamar yadda kuduri mai lamba 2065 na babban taron MDD ya tanada. Wannan ita ce halaltacciyar bukatar da Argentina ta gabatar na neman ikon mallakar tsibiran Falkland, kuma ya kamata kasashen duniya su ba ta goyon baya.
A zahiri, batun tsibiran Falkland a bayyane ya ke karara tun ba yau ba, kuma muhimmin abu shi ne, gadon tarihi na mulkin mallaka. Dalilin da ya sa bangaren Birtaniya ya ki ba da amsa shi ne, ba ya son ya bar moriyarsa da ba ta dace ba. Kwamitin kare hakkin bil Adam na MDD da kungiyoyin kasashen nahiyar Amurka da ma kasashe masu tasowa da suka hada da Sin, dukkansu sun sha nuna goyon baya ga Argentina wajen mayar mata da ikon mallakar tsibiran Falkland.
Bana shekaru 190 ke nan da Birtaniya ta mamaye tsibiran Falkland ba bisa doka ba. Tsohuwar “Daular da rana ba ta taba faduwa ba” ya kamata ta himmatu ta amsa bukatun shawarwari na Argentina tare da dawo mata da tsibiran Falkland ba tare da wani bata lokaci ba.
Zamanin mulkin mallaka ya shude har abada, kuma ikon mallakar tsibirin Falkland bai kamata ya zama matsala ta har abada ga jama’ar Argentina ba!(Safiyah Ma)