Ana gudanar da taron aiki na 2025 kan batun Taiwan daga yau Laraba zuwa gobe Alhamis. Zaunannen wakilin hukumar siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin wato JKS, kuma shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin CPPCC, Wang Huning, ya halarci taron tare da ba da jawabi.
Wang Huning ya bayyana cewa, ya kamata a tsaya tsayin daka kan manufar “kasancewar kasar Sin daya tak a duniya” da matsaya guda da aka cimma a shekarar 1992, da kuma yaki da ayyukan neman ’yancin kan Taiwan, da kiyaye hada kan kasar Sin. Dole ne a sa kaimi ga yin mu’amala da hadin gwiwa tsakanin babban yankin kasar da yankin Taiwan, da tallafawa ci gaban ’yan kasuwa da masana’antun Taiwan dake babban yankin, da kuma more damammaki da nasarorin da zamanantarwa irin ta Sin ta samu tare da ’yan uwa na Taiwan. Dole ne a samar da ingantaccen yanayi don matasa daga Taiwan su zo babban yankin don cimma burinsu. Dole ne a tsaya tsayin daka wajen adawa da dakile tsoma baki daga waje, da kuma karfafa yadda kasashen duniya suke bin manufar kasar Sin daya tilo. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp