A kasar Amurka, idan an ambaci sunan “kusa a kasuwar hannayen jari daga majalisar dokokin kasar”, za’a iya tunawa da shugabar majalisar wakilan kasar Nancy Pelosi da iyalanta.
Amma a hakikanin gaskiya, ba ita kadai da iyalanta ba, kana, ba daga majalisar dokokin kasar kawai ba ne, wato a fagen siyasar Amurka, ana iya samun kusoshi da dama a kasuwar hannayen jari.
Bayanan da aka fitar game da harkokin kudi na jami’an gwamnatin Amurka kimanin 12000 sun shaida cewa, daga shekara ta 2016 zuwa ta 2021, yawan takardun hannayen jari da sama da kaso 20 bisa dari na wadannan jami’ai suka mallaka ko suka yi cinikinsu, su kan karu ko ragu, daidai da kudirin ofisoshin ayyukansu.
Kusan wata daya da ya gabata, an wallafa hotunan sanatocin Amurka 97 a jaridar New York Times. Binciken jaridar ya nuna cewa, daga shekara ta 2019 zuwa ta 2021, cinikin takardun hannayen jari da wadannan sanatocin suka yi, ya yi daidai da ayyukan kwamitocinsu, wato, lokutan saye ko sayar da takardun hannayen jarin da suka yi, suna yin daidai da lokutan da majalisar dokokin Amurka ta binciki wasu kamfanoni, ko kuma aka bayar da wasu muhimman bayanai.
Ana kara samun ‘yan siyasar Amurka da suka zama manyan kusoshi a kasuwar hannayen jari, al’amarin da ya janyo rashin jin dadi daga al’ummar kasar.
Gazawar aikin dokoki, yana taimakawa ‘yan siyasar Amurka samun riba mai tsoka a kasuwar hannayen jari, daidai da labaran sirri da suka samu a wuraren aiki. Kana, gwamnatin kasar ba ta daukar matakai.
Sakamakon sabon binciken jin ra’ayin al’umma da kamfanin Gallup ya yi, ya nuna cewa, yawan al’ummar kasar Amurka da suka amince da majalisar dokokin kasar ya ragu warwas, har ya sauka zuwa kaso 7 bisa dari. (Murtala Zhang)