A cikin ‘yan kwanakin da suka gabata, wasu kamfanonin kera motoci na kasa da kasa sun sanar da cewa, za su kara zuba jari a kasar Sin, lamarin zai sa a kara habaka hadin gwiwar dake tsakanin Sin da sauran kasashen duniya.
Hakika babbar kasuwar kasar Sin dake cike da kuzari tana jawo hankalin kamfanonin ketare matuka. Kuma gabanin bikin gargajiyar kasar Sin wato bikin bazara, al’ummar Sinawa za su saye karin hajoji, kana a halin yanzu kasar Sin tana hanzartar raya sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko bisa fasahohin zamani, duk wadannan sun samar da karin damammaki ga kamfanonin ketare. Ban da haka, karuwar tattalin arzikin kasar Sin da manufar kara bude kofa ga waje ta kasar sun sa kamfanonin ketare karfafa imani kan makomarsu a kasar Sin.
Ana iya cewa, ko shakka babu kamfanonin ketare za su samu babbar riba bayan kokarin da suka yi a kasar Sin, sakamakon kyautatuwar tsarin tattalin arzikin kasar da babban bukatun cikin gida na kasar ta Sin. (Mai fassara: Jamila)