Masu jefa kuri’a a zaben gwamna da ‘yan majalisun jihohi a wasu wurare daban-daban na Jihar Bauchi sun yi korafin rashin fara aikin zabe da wuri.
Wakilinmu ya ziyarci rumfunan zabe da dama amma ba a fara aikin zaben a karfe 8:00am kamar yadda INEC ta yi alkawari ba.
- Tsokaci A Kan Sabanin Da Ake Samu Wurin Mu’amala
- ‘Yansanda Sun Cafke ‘Yar Shekara 53 Da Kayan Zabe A Legas
Da karfe 8:30am sa’ilin da muke zantawa da masu zabe a rumfar zabe ta Kofar Buri 2 Women Center da ke garin Kafin Madaki a karamar hukumar Ganjuwa, mazabar dan takarar Gwamnan Bauchi a karkashin NNPP, Halliru Dauda Jika sun nuna rashin jin dadinsu kan rashin fara aikin zaben da wuri.
Yusha’u Salisu, ya ce, “Mata da dattijai da mu duk mun fito tun 8am don jefa kuri’a amma har zuwa yanzu da nake magana da ku 8:30am babu wani ma’aikacin zabe ko jami’an tsaro da suka zo wannan rumfanar.
“Ko a zaben shugaban kasa da aka yi kwanaki sai karfe 10am ma’aikatan zaben nan suka zo. Kuma lallai ya kamata a gyara wannan matsalar,” ya yi korafi.
Wakilinmu ya ce hakan matsalar take a wurare daban-daban da ya zaga.