Ana sa ran yawan zirga-zirgar fasinjoji tsakanin biranen kasar Sin zai kai kusan miliyan 752.8 a ranaku uku na hutun bikin Qingming daga ranar 4 zuwa 6 ga watan Afrilu, kamar yadda alkaluma daga ma’aikatar sufuri ta kasar Sin suka nuna a yau Asabar.
An samu matsakaicin karuwar tafiye-tafiyen ta jiragen kasa da ta motoci a ko wace rana da ya kai kashi 75.3 da kashi 55.1 cikin dari bi da bi, idan aka kwatanta da makamancin lokaci na bara.
Bikin Qingming, wanda kuma aka fi sani da ranar share kabari, wani bikin gargajiya ne na kasar Sin don tunawa da kuma nuna girmamawa ga magabata. (Yahaya)