A yau Lahadi an kusan kai wa karshen lokacin hutu na kwanaki 7 na bikin kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin, saboda haka a garuruwa daban daban na kasar, an fara samun dimbin fasinjoji masu hawa jiragen kasa, da suke neman komawa gidajensu daga wuraren da suka yi ziyarar bude ido, inda ake sa ran jigilar fasinjoji 18,730,000 ta jiragen kasa a yau, lamarin da ya sa ake shirin fara aiki da karin jiragen kasa 1432. Kafin haka, a jiya Asabar, an yi jigilar fasinjoji kimanin 17,881,000 ta jiragen kasa a kasar Sin.
An ce, yawan zirga-zirgar mutane a lokacin hutun bikin kafuwar kasa na wannan karo, ya sa yawan fasinjoji masu hawa jirgin kasa a kasar Sin ya zarce miliyan 17 a kowace rana, cikin kwanaki 6 a jere. Inda aka gudanar da aikin jigilar wadannan fasinjoji lami lafiya, ba tare da wata matsala ba. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp