Sabon Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusif Gida-gida, ya bayyana cewa, sun karbi kundin mulkin jihar Mai dauke da bashin fiye da Biliyan 240.
Sai dai sabon gwamnan, ya sha alwashin binciko yadda aka yi Gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta ciyo bashin da kuma yadda aka tafiyar da dimbin bashin.
Gwamnan jihar Kano Mai jiran rantsuwa a yau Litinin 29 ga watan Mayun 2023 Engr. ya gabatar da jawabinsa cikin harshen turanci, inda ya godewa al’ummar jihar Kano bisa jajircewarsu wajen zabarsa tare da kyautatamasa zato.
Wakilinmu Freedom a fadar Gwamnatin Kano ya ruwaito cewar bayan karbar kundin mulki, Tawagar Gwamna sun zarce zuwa Filin wasa na Sani Abacha stadium da ke Kofar Mata a nan Kano inda za a rantsar da su.