Sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi ikirarin cewa APC ke ti mata bita da kulli, wanda suka kai kararta ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), domin a yi mata kiranye.
Idan za a iya tunawa dai, ‘yar majalisar da aka dakatar, wacce aka zabe ta a karkashin jam’iyyar PDP, ‘yan mazabarta ne ke da hakkin yi mata kiranye.
- Xi Jinping Ya Halarci Bitar Tawagar Lardin Jiangsu
- Hikimar Gwamnatin Jihar Jigawa Na Kaddamar Da Shirin Gina Rijiyoyin Burtsatsan Noman Rani
A baya-bayan nan ne INEC ta amince da karbar takardar yi wa ‘yan majalisar kiranye, amma ta nuna wasu batan bayanai game da masu shigar da kara.
A wata sanarwa da ta fitar, INEC ta ce an karbi bayanan da ba su kammala ba wadanda suka hada da adireshi da lambobin wayar wadanda suka shigar da karar.
Da take jawabi ga taron jama’a wadanda suka yi mata kyakkyawar tarba a lokacin da ta dawo gida, ‘yar majalisar ta zargi INEC da taimakawa tare da jagorantar masu shigar da kara don ba su damar kammala ayyukansu na haram.
Ta ce, “Abin da nake gani shi ne, INEC na taimaka wa masu shigar da kara kan yadda za su kammala ayyukansu na haram.
“Wannan shi ne karon farko da aka gabatar da koken, ba su da adireshi, lambobin waya, duk da hana amma INEC ta shiryar da su yadda za su gabatar da bayanan da za su kammala kokensu.
“Masu shigar da kara, ‘ya’yan jam’iyyar APC a yanzu suka mika takarda mai dauke da adireshin da babu shi domin ganin an yi min kiranye.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp