Shugaban hukumar zabe ta jihar Sakkwato, Aliyu Sulaiman, a ranar Litinin ya bayyana jam’iyyar APC a matsayin wadda ta lashe zaben dukkanin kananan hukumomi 23 da aka gudanar a ranar Asabar.
Bugu da kari, APC ta lashe dukkanin kujerun kansiloli a zaben wanda jam’iyyu 15 suka shiga, sai dai babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta kauracewa shiga zaben.
- Ƴan Ta’adda Sun Lalata Wutar Lantarkin Maiduguri Zuwa Damaturu
- Ɗan takarar APC, Ya Lashe Zaɓen Gwamnan Jihar Edo
Jim kadan da bayyana sakamakon, hukumar zaben ta jihar, ta bai wa zababbun shugabannin kananan hukumomi takardar shaidar lashe zaben.
LEADERSHIP ta samu labarin cewa, Gwamna Ahmed Aliyu zai rantsar da sababbin shugabannin a fadar gwamnatin jihar a yammacin yau, Litinin, 23 ga watan Satumba.