A daidai lokacin da gwamnatin tarayya ke kokarin kawo karshen biyan tallafin kudade a bangaren wutar lantarki, rahoto da ke fitowa daga hukumar kula da wutar lantarki ta Nijeriya (NERC) ya nuna cewa masu amfani da wutar lantarki a jihohim Adamawa, Borno da Yola ne za su biya kudin wuta mafi tsada.
A cewar rahoton shekara-shekara na 2024 da NERC ta fitar, jihohin wadanda suke karkashin kamfanin rabar da wutar lantarki ta Yola (YEDC) za sha wuta ne kan naira 266.64 kan kowace kilowattn guda (kwh).
- ‘Yan Nijeriya Miliyan 40 Ke Fuskantar Barazanar Kwararowar Hamada – Ministan Muhalli
- Firaministan Sin Ya Jagoranci Taron Tattaunawa Tsakanin Shugabannin Sin Da EU Karo Na 25 Tare Da Shugaban Majalisar EU Da Shugabar Hukumar EU
Rahoton ya ce, yawan kudin ya faru ne sakamakon tsadar kayan aiki da kuma wasu abubuwa na musamman (kamar barnata da kayan wuta da rashin tsaro a sassan yankin), wanda gwamnatin tarayya ta amince da shi a matsayin wani bangare na yunkurin mayar da hannun jari a shekarar 2021.
Wannan matakin dai na zuwa ne kan yawan kudin tallafin da ake sanyawa a sashin, da zarar gwamnati ta cire tallafin yankin zai biya kudin wuta mafi tsada.
Sai dai, rahoton ya ce Ikeja da Eko DisCos suna da rahusa a sabon farashin wuta da kuma kaso na tallafin da ake bayarwa kowace sashe na makamashin da ake bayarwa.
“A matakin kasa, matsakaicin CRT ya kasance naira 175.31 a kowace kWh, yayin da matsakaicin kudin wuta da aka yarda ya kasance naira 100.27/kWh, wanda ya haifar da matsakaicin adadin kudin tallafi naira 75.04/kWh.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp