Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal wadda Mikel Arteta ke jagoranta ta kafa tarihin jefa kwallaye 7 rigis a waje, a wasan da ta doke abokiyar karawarta PSV da ci 1-7 a filin wasa na Philips Stadion dake Endhoiven.
Hakazalika, wasan shi ne na farko a cikin shekaru 13 da Arsenal ta jefa kwallaye 7 a ragar abokan karawarta, tun bayan da ta taba cin Newcastle 7-3 a gasar Firimiya.
- ‘Yan Fashi Da Makami Sun Kashe Tsohon Babban Kwanturolan Hukumar NIS A AbujaÂ
- Dorawa Wasu Laifi Ba Zai Kawo Ci Gaban Da Amurka Ke Muradi Ba
Jurien Timber, Nwaneri, Mikel Merino, Martin Odegaard, Trossard da Califiori ne su ka jefawa Gunners din kwallaye 7 a ragar PSV, Arsenal wadda ta kasa jefa kwallo ko daya a wasanni biyu na baya bayan nan a gasar Firimiya, ba ta yi tsammanin samun nasara irin wannan a gasar Zakarun Turai ba.
Kocin Arsenal Mikel Arteta ya bayyana farin cikinsa akan wannan tarihi, inda yace abu mafi muhimmanci shi ne ganin cewar Arsenal na da babbar damar tsallakawa zuwa matakin na kusa da na kusa da na karshe duk da cewar akwai jan aiki idan PSV ta ziyarci Arsenal a gidanta inji Arteta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp