Arsenal ta kammala sayen tsohon mai tsaron ragar Chelsea, Kepa Arrizabalaga, bayan ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru uku a ƙungiyar.
A kakar da ta gabata, Kepa ya buga wasanni 35 a matsayin aro a Bournemouth.
- David Mark Da Aregbesola Sun Zama Shugaba Da Sakataren Jam’iyyar ADC
- Tawagar Gwamnatin Tarayya Da Ɗangote Sun Halarci Jana’izar Aminu Ɗantata A Saudiyya
“Na yi matuÆ™ar farin ciki da zuwa Arsenal. Ina fatan samun nasarori tare da Æ™ungiyar,” in ji Kepa, É—an kasar Sifaniya mai shekaru 30.
Har yanzu Kepa shi ne golan da aka fi kashe kuÉ—i wajen siya a duniya, inda Chelsea ta biya fam miliyan 71 don É—aukarsa daga Athletic Bilbao a shekarar 2018.
Zuwa Arsenal na iya zama ƙalubale ga David Raya, wanda ke matsayin golan farko yanzu.
A kakar da ta wuce, Arsenal ta karɓi Neto a aro daga Bournemouth domin taimaka wa Raya, amma yanzu ta yanke shawarar dawo da shi domin ɗaukar Kepa daga Chelsea.
Kepa ya buga wasanni 163 a Chelsea, kuma yana cikin tawagar da ta lashe kofin zakarun Turai, Europa League da kuma kofin ƙungiyoyin duniya (Club World Cup).
Haka kuma, ya shafe shekara guda a aro a Real Madrid, inda ya taimaka musu suka lashe Laliga da Champions League a kakar 2023-24.
Chelsea ta É—auki Kepa ne a 2018 bayan kasa É—aukar Thibaut Courtois daga Atletico Madrid da Alisson Becker wanda ya koma Liverpool.
Daga baya kuma ta gane cewa bai cancanci kuɗin da aka kashe a kansa ba, ciki har da albashin fam 190,000 da yake karɓar duk mako.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp