Arsenal ta kammala sayen tsohon mai tsaron ragar Chelsea, Kepa Arrizabalaga, bayan ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru uku a ƙungiyar.
A kakar da ta gabata, Kepa ya buga wasanni 35 a matsayin aro a Bournemouth.
- David Mark Da Aregbesola Sun Zama Shugaba Da Sakataren Jam’iyyar ADC
- Tawagar Gwamnatin Tarayya Da Ɗangote Sun Halarci Jana’izar Aminu Ɗantata A Saudiyya
“Na yi matuƙar farin ciki da zuwa Arsenal. Ina fatan samun nasarori tare da ƙungiyar,” in ji Kepa, ɗan kasar Sifaniya mai shekaru 30.
Har yanzu Kepa shi ne golan da aka fi kashe kuɗi wajen siya a duniya, inda Chelsea ta biya fam miliyan 71 don ɗaukarsa daga Athletic Bilbao a shekarar 2018.
Zuwa Arsenal na iya zama ƙalubale ga David Raya, wanda ke matsayin golan farko yanzu.
A kakar da ta wuce, Arsenal ta karɓi Neto a aro daga Bournemouth domin taimaka wa Raya, amma yanzu ta yanke shawarar dawo da shi domin ɗaukar Kepa daga Chelsea.
Kepa ya buga wasanni 163 a Chelsea, kuma yana cikin tawagar da ta lashe kofin zakarun Turai, Europa League da kuma kofin ƙungiyoyin duniya (Club World Cup).
Haka kuma, ya shafe shekara guda a aro a Real Madrid, inda ya taimaka musu suka lashe Laliga da Champions League a kakar 2023-24.
Chelsea ta ɗauki Kepa ne a 2018 bayan kasa ɗaukar Thibaut Courtois daga Atletico Madrid da Alisson Becker wanda ya koma Liverpool.
Daga baya kuma ta gane cewa bai cancanci kuɗin da aka kashe a kansa ba, ciki har da albashin fam 190,000 da yake karɓar duk mako.