A yau dai ga: $1 = N1652, £1 =N2010, €1 = N1985
To, idan ba ka san tushen matsalolinmu a yau ba, ka dauki lokaci ka karanta abubuwan da ke nan kasa:
Shekara 42 da suka gabata, a ranar 25/07/1980 daidai, sauyin kudin Nijeriya ya kasance ne a: $1 = 0.80k
Ka yi mamaki?
To, a 1980 mun fi yawan aiki da kere-kere fiye da yadda muke a yau.
Abubuwan da suka haifar da ci gaban tattalin arziki a shekarar 1980 sun hada da:
Muna fitar da man fetur da aka tace zuwa kasashen waje. A yau muna shigo da dukkanin man fetur da aka tace.
Muna hawa motoci, bas-bas da manyan motoci da aka hada a cikin gida. Motocin ‘Peugeot’ a Kaduna da motocin ‘Bolkswagen’ a Legas.
Leyland suna samar da manyan motoci da bas-bas a Ibadan kuma ANAMCO a Inugu suna samar da manyan motoci da bas-bas.
Steyr a Bauchi suna samar mana da tarakta na aikin gona. Kuma ba kawai hada motocin ake yi ba, ana kera yawancin sassan motoci:
Bono Products a Legas suna kera kujerun motoci.
Edide a Ibadan suna kera batir ba kawai ga Nijeriya ba, har da dukan yankin Yammacin Afirka.
IsoGlass da TSG a Ibadan suna kera gilashin motoci.
Ferrodo a Ibadan suna kera pad din birki da diski.
Dunlop suna kera tayoyi a Lagos kuma Michelin suna kera tayoyi a Port Harcourt. Kuma tayoyin suna fitowa daga gonakin roba da ke a Ogun, Bendel da Jihar Ribas.
Muna sauraron rediyo da kallon talabijin da aka hada a Ibadan daga Sanyo.
Muna amfani da firij, firiza da injin sanyaya iska da aka kera daga Thermocool da Debo.
Muna sanya kayan da aka kera daga masana’antar UNTL Tedtile Mills a Kaduna da Chellarams a Legas. Ba daga auduga da aka shigo da ita daga waje ba, daga auduga da aka shuka a Nijeriya suke.
Ruwan mu yana gudana a cikin bututun da aka kera daga Kwalipipe a Kano da Duraplast a Legas.
Bahaya muna amfani da tanda da aka kera daga Kano da Abeokuta.
Muna dafa abinci da iskar gas da aka ajiye a cikin kwalin gas da aka kera daga kamfanin NGC a Ibadan.
Wutar lantarki tana gudana ta cikin wayoyi da aka kera daga Nijeriya Wire and Cable, Ibadan; NOCACO a Kaduna da Kablemetal a Legas da Port Harcourt.
Muna sanya takalman da Bata da Lennards Stores suka kera. Takalman ba daga fata da aka shigo da ita daga waje suke ba, daga fata da aka tanada a Kaduna suke.
Muna tashi cikin jiragenmu na kasa, (Nigeria Airways), zuwa yawancin wurare a duniya. Nigeria Airways yana cikin manyan jiragen Afirka a lokacin.
Yawancin abincin da muke ci a lokacin ana nomansa a Nijeriya.
Muna samar da duk wadannan da sauran su a shekarar 1980.
A yau, muna shigo da kusan komai daga waje. Wannan ba abin tsoro ba ne?
A nan ne tushen matsalar sauyin kudi mara kyau da muke fama da shi a yau, kuma kowane daya daga cikin mu na da rawar da zai taka wajen gyara wannan mummunan yanayi.
Mun dade muna magana kan wadannan matsalolin da sauran su.
Bai ishe mu mu rika korafi game da sauyin kudi ba ko zargin abin da wasu ba su yi ba ko suke kasa yi. Manyan tambayoyin sune:
Me muke samarwa yanzu?
Wace rawar ne ‘yan siyasar mu na yanzu suke takawa?
Duk da haka, muna guje wa alhakin da ke kanmu, alhali kuwa idan ba mu fuskance ta ba, ba za ta tafi ba. A maimakon haka za ta kara tsananta.
Ga ‘yan siyasa, idan ba ku da karfin gyara Nijeriya ta koma irin yadda take a shekarar 1980, to ku zauna a gida kada ku bata mana lokaci.
Duk mu koma gona ko kankantar sa.
Wassallam.