Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Aston Villa ta kammala ɗaukar tsohon ɗan wasan Real Madrid Marco Asensio daga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta PSG a matsayin aro zuwa ƙarshen kakar wasa ta bana.
Asensio wanda ya bar Real Madrid a shekarar 2023 ya na ɗaya daga matasan ƴan wasa da tauraruwarsu ke haskawa a harkar ƙwallon ƙafa a yanzu.
- PSG Na Neman Dauko Lamine Yamal Daga Barcelona A Kan Yuro Miliyan 200
- Wannan Ita Ce Shekarata Ta Karshe A PSG —Mbappe
Aston Villa ta wallafa a shafinta na kafar sadarwa cewa Asensio ya rattaɓa hannun komawa ƙungiyar a matsayin aro daga PSG har zuwa ƙarshen kakar wasa ta bana.
Asensio ne ɗan wasa na biyu da Villa ta ɗauka aro bayan Marcus Rashford wanda ta aro daga Manchester United yayin da ake gab da rufe kasuwar saye da sayarwar ƴan ƙwallo a nahiyar Turai.