Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano ya tabbatar wa jama’ar Jihar Kano cewa, asibitin yara na Hasiya Bayero, zai koma bakin aiki nan da makonni biyu masu zuwa.
Ginin asibitin yana daya daga cikin gine-ginen da gwamnatin kwato daga hannun wanda gwamnatin Abdullahi Ganduje ta mallakawa a cewar gwamnatin mai ci.
- NLC Za Ta Yi Zama Kan Hana Wasu Ma’aikatan Kano Albashi
- Gwamnatin Kano Za Ta Bincike Dakatar Da Albashin Ma’aikatan Kano
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mukaddashin sakataren yada labaran gwamnan Jihar, Malam Hisham Habib, ya fitar a Kano ranar Lahadi.
Yusuf ya bayyana haka ne a Kano a lokacin da ya karbi bakuncin Sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir, wanda ya kai masa ziyarar Sallah.
Gwamnan ya umarci kwamishinan lafiya, Dr. Abubakar Labaran, da ya yi aiki ba dare ba rana domin ganin an dawo da asibitin aiki.
Gwamnan ya ba da tabbacin cewa gwamnati mai ci za ta ci gaba da ba da fifiko a bangaren kiwon lafiya don tabbatar da manufofinta na bunkasa fannin lafiya a fadin jihar.
Gwamnan ya nuna damuwarsa kan yanayin tsaftar muhalli a jihar, ya nanata kudurin gwamnatinsa da Jam’iyyar NNPP ke jagoranta na tsabtace muhalli.
Gwamnan ya kalubalanci masu suka da su rika ajiye bayanan aikinsa, su kuma yi masa hukunci bayan ya kammala wa’adinsa, yana mai tambayar dalilin da ya sa duk wani mai mulki zai iya kwace dukiyar jama’a ya mayar da ita don amfanin kansa.
Tun da farko, Abdulkadir ya shaida wa gwamnan cewa majalisar masarautar ta kafa kungiyar ‘yan banga don inganta tsaro da zaman lafiya a tsakanin mazauna yankin.