Wani bincike ya nuna cewa, Asusun ajiyar Nijeriya na kasar wajen ya ragu da Dala biliyan biyu, a 2025.
Wannan binciken wanda Jaridar BusinessDay ta gudanar a Babban Bankin Nijeriya CBN.
- Nazarin CGTN: Manufar Sanya Muradun Amurka Gaba Da Komai Na Lalata Dangantakar Dake Tsakaninta Da Turai
- Yadda Ake Ayyukan Gina Ababen More Rayuwa A Jihar ZamfaraÂ
A cewar wasu alakakuma da suka fito daga Babban Bankin Nijeriya CBN, sun nuna cewa, a ranar 2 ga watan Janairun 2025, Asusun ya kai matakin Dala biliyan 40.883, amma Asunsun, ya yi matkar raguwa zuwa Dala biliyan 38.880 a ranar 17, ga watan Fabirairun 2025.
Kazalika, Nijeriya a 2024, bashin da kasar ketare da ake bin kasar, ya karu zuwa Dala 3.8, inda kuma bashin cikin gida ya kai Dala miliyan 900, da kuma wasu basussukan Dala biliyan 2.2 sai kuma bashin Dala miliyan 750 wanda ya kasance daga cikin bashin Dala biliyan na rancen da da Gwamnatin kasar ta karbo, daga gun Bankin Duniya.
Bugu da kari, alkaluman na CBN sun nuna cewa, kadarorin Nijeriya na waje sun ragu.
Wasu alkaluma da suka fito daga Babban Bankin Nijeriya CBN sun suna cewa, a 2024, Asusun ajiyar Nijeriya rufe ne a kan Dala biliyan 40.877.
Wani masani a fannin tattalin arziki da ke da zama a jihar Legas Ibukun Omoyeni, a wani hasashe da ya yi kan shekarar 2025 ya bayyana cewa, Nijeriya ta fuskanci wasu bin ka’dojin yarjejeniyar karbar bashi, inda ya kara da cewa, baya ga batun kafin a shiga shekarar 2026, akwai wasu basussuka na waje Nijeriya ta ciwo wandanda kuma, ba su riga sun gama nuna ba, wanda akalla zai iya kai wa Dala biliyan 1.33 a duk shekara ko kuma sama da haka wadanda suka hada da biyan kudin ruwa na rancen, inda mai yuwa, da ya kai akalla, Dala biyan 2.24, wanda kuma zai iya wuce na gajeren zango .
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp