Dalibai a jami’o’in gwamnati yanzu suna tururuwar neman gurbin karatu a jami’o’i masu zaman kansu saboda yajin aikin da mambobin kungiyar malaman jami’o’in Nijeriya ASUU ke yi.
Mataimakin shugaban jami’ar Al-Hikmah da ke Ilorin a jihar Kwara, Farfesa Nuhu Yusuf ne ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai da ya kira a taro karo na 12 da aka gudanar a dakin taro na Ivory Tower.
A ranar Asabar mai zuwa ne jami’ar za ta yaye dalibai 1,280, daga cikinsu akwai 25 da suka lashe lambar yabo ta farko (first class) a zangon karatu na shekarar 2021/2022.
“Jami’o’i masu zaman kansu suna samun karuwar dalibai daga jami’o’in gwamnati saboda kalubalen da ke addabar bangaren gwamnati da kungiyar Malaman Jami’o’i ASUU.
Ya kara da cewa “A jami’ar Al-Hikmah mun samu karuwar daliban jami’o’in gwamnati dake bukatar guraben cigaba da karatunsu a wurin mu sabida muna da tsayayyar tsarin karatu,” in ji farfesa Nuhu Yusuf.