Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa, ASUU za ta maka gwamnatin tarayya a gaban kotu kan rijistar da ta yi wa sabbin kungiyoyin malaman jami’o’i wato CONUA da NAMDA.
Lauyan kungiyar ASUU, Femi Falana, shi ne ya bayyana haka a wata hira da yayi da tashar talabijin ta Channels a ranar Alhamis, inda ya ce, za su kalubalanci yi wa kungiyoyin biyu rijistar.
A ranar Talata ne ministan kwadago, Chris Ngige, ya bayar da takardar shedar rijista ga sabbin kungiyoyin biyu da ke matsayin kishiyoyi ga ASUU.
A lokacin da yake ba su takardar Ngige, ya ce kungiyoyin biyu za su wanzu kafada da kafada da ASUU. BBC Hausa ta rahoto.
Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa, ASUU ta fara yajin aiki ne tun ranar 14 ga watan Fabrairu kan wasu alkawura da take zargin gwamnatin ta gaza cika mata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp