A ranar Asabar din da ta gabata ne shugabannin kasashen kungiyar Tarayyar Afirka AU, suka zabi shugaban kasar Angola Joao Lourenco, a matsayin sabon shugaban karba-karba na kungiyar da kuma ministan harkokin waje da hadin gwiwar kasa da kasa na Djibouti, Mahamoud Ali Youssouf, a matsayin sabon shugaban hukumar gudanar da ayyukan kungiyar, wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula a kasashe biyu masu matukar muhimmanci a nahiyar, wato Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo (DRC) da kasar Sudan. Rikicin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo na kara kamari, bayan samun galaba a wasu yankunan kasar da ‘yan tawayen M23 suka yi, na baya-bayan nan shi ne kwace iko da muhimman wurare da dama a birnin Bukavu, hedkwatar lardin Kivu ta kudu, da safiyar ranar Asabar, ciki har da gidan gwamnan lardin, makonni biyu bayan kwace babban birnin Goma. DRC dai ta zargi kasar Rwanda da marawa ‘yan tawayen baya, amma Rwanda ta musanta wannan zargin. Tun daga wannan lokacin kawo yanzu, shugabannin nahiyar ba su daina yin kiraye-kiraye da a tsagaita wuta ba tare da wani sharadi ba, da dakatar da tashin hankali da kuma bude manyan hanyoyin samar da kayayyaki da filin jirgin Goma ba. Hakazalika, Sudan ita ma ta kasance wata babban jigon tashe-tashen hankula da shugabannin nahiyar ke tattaunawa. Tsananin wadannan rikice-rikice na iya haifar da yakin yanki, ganin cewa sojojin kasashe makwabta, kamar Afirka ta Kudu sun riga sun shiga kasar Congo Kinshasa. Idan ba mu manta ba, tun bayan manyan yake-yake guda biyu wadanda suka faru tsakanin 1996 zuwa 2003, wanda ya hada da kasashe kusan goma na Afirka, ake zaman dar-dar a gabashin Congo Kinshasa, wanda kuma ke barazanar sake haifar da rikicin kabilanci da na siyasa a yankin manyan tabkuna.
Kungiyoyin kasa da kasa da masu ruwa da tsaki sun yi gargadin cewa idan ba a yi taka tsantsan ba, wannan rikici na iya rikidewa zuwa yakin yanki, sun nakalto bakar azabar da aka fuskanta a tashe-tashen hankulan shekarun 1990. Hakazalika, al’ummar kasa da kasa na fatan sabon shugabancin AU zai dauki kwararan matakai da inganta hadin gwiwa, don kwantar da hankula, da samar da kyakkyawan martani ga duk wani rikicin da ke addabar nahiyar.