Kungiyar Tarayyar Afirka, (AU) ta zama mamba ta dindindin a rukunin kasashe 20 mafi arziki da tasiri a duniya (G20).
Firaministan Indiya, Narendra Modi, ya sanar da shigar ta AU din a taron G20 da aka gabatar a New Delhi.
- Taron G20 Ya Yi Kira Da A Inganta Hadin Kai Don Tinkarar Kalubaloli Tare
- Firaministan Kasar Sin Ya Halarci Zaman Mataki Na Farko Na Taron Koli Na 18 Na Shugabannin Kasashen G20
A jawabinsa na bude taron, firaministan kasar Modi ya mika goron gayyata ga kungiyar tarayyar Afrika da shugabar kungiyar Azali Assoumani ta wakilta, don samun kujerar dindindin a tsakanin shugabannin kasashen na G20.
Wani daftarin sanarwar da aka fitar a baya ya bayyana cewa, “Muna maraba da kungiyar Tarayyar Afirka a matsayin memba ta dindindin a G20, kuma mun yi imani da cewa shigar Kungiyar Tarayyar Afirka cikin G20, zai bayar da gudummawa sosai wajen magance kalubalen duniya a wannan zamanin.”
Firayim Minista Modi ne ya gabatar da wannan shawarar mai cike da tarihi a cikin watan Yuni kuma ya zama wani muhimmin ci gaba a cikin ayyukan Tarayyar Afirka a duniya.
Sauran muhimman batutuwan da ake la’akari da su yayin taron sun hada da kara bayar da lamuni ga kasashe masu tasowa ta cibiyoyi da dama, da yin kwaskwarima kan tsarin basussuka na kasa da kasa, da ka’idojin da suka shafi hada-hadar cryptocurrencies, da tasirin abubuwan da ke faruwa a fannin siyasa kan tsaron abinci da makamashi.