Manzon rahma (SAW) ya koyar da wani rigakafin da idan mutum ya yi zai kara samun intacciyar lafiya a jikinsa, shi ne, kada mu zauna ba aure, lallai idan mutum yana da hali ya yi aure, domin ya fada wa sahabbansa cewa wanda duk ya samu a cikinku ya yi aure.
Hadisi ne ingantacce da yake cikin Bukhari da Muslim, domin auren nan zai samar masa kariya, wanda bai samu damar yin auren ba aka ce ya yi azumi don ya rage masa karfin sha’awa, saboda maniyyi yana da matsala idan yana tarar wa mutum, gashi kuma an haramta maka yin zina, kuma kuma kai ma ka san illolin da yake cikinta, kuma kai istimna’i nan ma ka jawo wa kanka, wato shi ne mutum ya yi ta wasa da gabansa har ya biya bukatarsa.
- Wakilin Sin A Taron Vienna Ya Soki Lamirin Yarjejeniyar AUKUS
- Masana Da Jami’an Kasashen Sin Da Tanzania Sun Sha Alwashin Inganta Hadin Gwiwa Tsakanin Kasashe Masu Tasowa
Wannan yana kankantar da gaba, kuma yana sa raunin zuciya, mai yin wasa da gabansa ba ya samun karfin zuciya. Saboda haka mafita kawai ita ce aure, duk wanda zai zo ya rika yi maka wata huduba cewa ai kai matashi ne ka bari sai ka yi Digiri ko wani abu, wannan mai baka shawarar mahaukaci ne yana so ne ya raba ka da koyarwar Manzon Allah, kuma wannan din da ya hana ka aure shi zai zo ya ce ku je ku yi zina, a she makaryaci ne ya kai ka ya baro.
Ka je ka bincika ka ga shugabannin duniyan da kake ji Yahudawan da Nasara a shekara nawa suke aure? In ban manta ba George Bush na farko yana da shekaru ishirin ya yi aure. Amma kuma suna ta yada jita-jitar kada a yi aure da wuri, za ka samu irin su Obama ga su nan da ‘ya’ya manya-manya saboda sun yi aure da wuri.
Don haka yin aure da wuri lafiya ce ga jikin mutum, yana sanya jikin mutum ya samu cikakkiyar lafiya, kuma rigakafi ne ga talauci. Da yawa wadanda suka yi kudi idan ka duba za ka ga sai da suka yi aure suka samu dukiya ko rufin asiri. Sannan kuma wani rigakafin ga mata su ma Manzon Allah ya ce su rika rufe jikinsa, don gudun kada a yi musu fyade, rigakafi ne ga jikinsu da yake hana aljanu shiga jikinsu. Idan muka duba za mu ga kasar da tafi karancin yi wa mata fyade a duk duniya Saudiya ce, sai irin makwaftansu Oman da sauransu, sirrin shi ne matansu gaba daya a rufe suke. Ba a ce ba sa yin wani abu mara kyau ba, amma a boye ake yi.
Saboda mutum ya ci abinci ya koshi, dole sha’awa ta zo masa, amma kuma abin da zai motsa sha’wara an boye shi, saboda kafin ya gani sai ya sha wahala. To amma mace ta bude jikinta ta bayyanar da wasi abubuwa nata, da mutum ya gani sai abin ya motsa masa sha’awa, in tsautsayin bai fada kanta ba zai iya fada wa kan wata.
 Da ya samu dama a kanta koda yarinya ce karama sai ya afka mata, ga laifuffuka nan na fyade ana ta samu, ga shi nan ana ta fada a labarai, dan shekara kaza ya yi wa yarinya karama fyade. Msali a ce dan shekara saba’in ya yi wa ‘yar shekara shida fyade, kaga ai ba ita ya kalla ba, amma wadda ta yi shigar ita ya kalla sha’awarsa ta motsa. Amma saboda ba zai iya samunta ba ko don rashin kudi ga tsufa, kuma ga matan nan manya-manya sun ki su yi aure, wasu suna son yin auren amma iyaye sun ki yi musu an ce sai sun yi karatu. Kuma suna cudanya da maza baligai a makarantu, suna bayyana jikinsu iyakar bayyana wa da shiga ta badala da iskanci.
Ga lamarin yana faruwa an rasa maganinsa, kullum ka ji an ce an kai mutum kaza kotu an yanke masu hukuncin shekara kaza, a gidan yari. To in za a yanke wa mutum shekara dubu in ya fito sai ya sake in dai mata ba su daina shigar banza ba.
Sannan Manzon Allah SWA ya hana mu cin abinci da hannun hagu domin rigakafin kamuwa da cuta, domin hannun hagu shi ake sawa a kazanta, don haka duk abin da mutum zai ci ya tabbata ya ci da hannun dama. Sannan ya koya mana nisantar kamuwa da annobar ciwo, cewa idan mutum yana da dama ya lashi zuma sau uku a jere da sassafe kafin mutum ya ci komai, idan aka ce sabon wata ya kama tun daga farkon watan Musulunci kafin ya kai 15 ake son ka yi, kwana uku a jere, sannan ka lasa wa yaranka suma sau uku kwana uku a jere.
In Allah ya so ka yi musu haka, to annobar da za ta zo a wannan shekara Allah za tsare su. Sannan yana daga cikin koyarwar da Malamai suka yi mana na rigakafi, mutum ya rubuta Fatiha kafa bakwai da kursiyyu bakwai da lakad ja’akum kafa bakwai, Falaki bakwai Nasi bakwai, a rubuta da tawada mai kyau a allo mai kyau a wanke da ruwa mai kyau. Ruwan da za a wanke in an samu Zamzam an fi son haka, in ba’a samu ba an fi son ruwan Sama, in ba’a samu ba a sa ruwan rijiya. In babu kuma to sai a nemi kowa ne ruwa, sai a wanke a sha shi ma ya wadatar, domin shi Allah niyya yake kallo.
Sannan ana rubuta Ayatusshifa’a din nan guda shida da suke cikin Alkur’ani su ma a rubuta duk wata a sha a gida, wannan ma ana fatan samun kariya daga annoba, wannan fa ba wai an ce idan cuta ta kama ka za ka warke ba ne, a’a rigakafi za ka yi yadda cutar ma ba za ta kama ka ba.
Sannan Manzon Allah SAW ya hana mutum ya yi kaki ya tofar a Masallaci, Malamai likitocin Musulunci suka ce ai saboda Masallaci wurin taruwar jama’a ne, idan ka yi tana iya yiwuwa kana da wata cuta da ta kama ka a huhunka idan ka tofar, iska za ta iya dauka ta sanya wa mutane.
Sannan Manzon Allah ya ce, ku ji tsoron la’ana guda biyu, kamar yadda ya zo a ruwayar Muslim, ya ce la’ana ta farko ita ce, mutum ya yi ba-haya a kan hanyar da mutane suke wucewa, ko a inuwar bishiya. Hikimar hanawar ita ce, iska za ta iya daukar cutar da ke cikin wannan najasa taka ta kai wa mutane.
Bincike ya nuna cutar kwalara bayan garin da ake yi ne iska take daukar sa ta kawo cikin mutane sai a shaka, ko ta zuba acikin ruwa sai a yi abinci da shi ko a sha, sai a yi ta amai ana gudawa. Kamar a kauyuka yadda za ka ga ana haduwa ana wanka a wuri daya, kuma ruwan nan wani fa ba ya gudu, a ciki za a yi fitsari ko a wanke bayan gari. Manzon Allah SAW ya hana mu fitsari a cikin ruwa, sai kare lafiyarmu, to suna da yawa a yanzu dai mun fadi kusan guda ishirin da biyu a iya dan bayanin nan da muka yi.
Allah ta’alah ya yi wa abin da muka ji albarka, wassalamu alaikum wrahmatullahi Ta’alah wabarkatuhu.