An kama wani dan Nijeriya mai suna Johnson a Birnin Delhi bisa laifin damfarar wata ‘yar kasar Indiya daga Rajnandgaon, Chhattisgarh da karyar zai aure ta.
‘Yansandan Rajnandgaon sun cafke Johnson, wanda ake zargi da damfarar matar da ke da lakhs din kudi bisa zargin yin aure.
- Kasar Sin Ta Yi Kira Da A Hada Karfi Da Karfe Wajen Samar Da Yanayin Da Zai Dace Da Warware Matsalar Sudan
- EU Ta Ware Euro Miliyan 1 Don Tallafa Wa Wadanda Ambaliyar Ruwa Da Kwalara Suka Shafa A Nijeriya
‘Yansanda sun bayyana cewa Johnson yana zaune a Delhi a asirce, tun bayan karewar biza da fasfo dinsa.
A cewar ‘yansandan, wanda ake zargin ya kirkiro bayanan karya a shafin intanet auren inda kuma aka jera bayanan wanda aka kashe.
Da farko ya ja hankalin matar kuma ya tabbatar mata da cewa shi dan kasuwa ne da ke zaune a Birtaniya yana shirin fadada kasuwancinsa zuwa Indiya.
Ana zargin wanda ake tuhumar ya tuntubi matar ne ta hannun abokinsa, inda ya ce ya makale a filin jirgin saman Delhi kuma yana bukatar kudi don musayar kudin Burtaniya da yake da shi.
Rahul Deb Sharma, Sufeto na ‘yansanda a Rajnandgaon, ya ce, “Ya ci zarafin matar kuma ya yaudare ta Rufee 15,72,000 (kimanin Naira 9,100,000) tare da taimakon abokin aikinsa.”
Daga baya, lokacin da wacce aka damfara ta yi kokari ta kira shi, ta ji wayarsa a kashe.
Da ta fahimci cewa an yi mata zamba ne, matar ta kai kara hukumar ‘yansandan Dongargarh da laifin zamba.
“Mun fara bincike kan korafin mai bukata. Tare da taimakon wani rukunin intanet, an gano cewa wanda ake zargin yana zaune a Delhi. Kungiyarmu ta kai farmaki a gidansa na Delhi inda ta kama shi, “in ji Sharma.
“Wanda ake zargi Johnson mazaunin Nijeriya ne. Ya yaudari ‘yan mata da yawa ya zuwa yanzu. Muna kokarin samun karin bayani ta hanyar tambayoyi.”
‘Yansandan sun kuma lura cewa Johnson yana kusa da shekaru 40. Hukumomi sun kwato kwamfutar tafi-da-gidanka da wayoyin hannu hudu daga hannun wanda ake zargin, kuma an kulle asusun ajiyarsa na banki.