Babban Jami’in Diflomasiyya Na Kasar Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Jamhuriyyar Congo
Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi ya tattauna da takwaransa na Jamhuriyar Congo da kasashe masu amfani da harshen Faransanci, kuma Jami’i dake kula da ’yan Congo mazauna kasashen waje, Constant-Serge Bounda a jiya Alhamis, a Beijing babban birnin kasar Sin. A jawabin da ya gabatar, Wang ya yi kira ga bangarorin biyu da su yi kyakkyawan shiri game da taron kungiyar ministoci kan alakar hadin gwiwa tsakanin Afrika da Sin, wanda aka shirya gudanarwa a kasar Congo a shekara mai zuwa. Ya kuma kara da cewa Sin a shirye take ta yi aiki da kasashen Afrika, domin gina tsarin jagorancin duniya na gaskiya da adalci bisa daidai da muradun bai daya na kasashen kudancin duniya. A nasa jawabin Bounda ya ce, jamhuriyyar Congo, na goyon bayan jerin shirye-shiryen hadin gwiwa na duniya da kasar Sin ta bijiro da su, tare da tabbatar da cikakken goyon bayanta ga ka’idojin Sin. Ya kara da cewa, jamhuriyyar Congo na yabawa kasar Sin bisa gudummawar da take bai wa Afrika a fannin kula da lafiya, da taimakon da take ba ta, wajen yaki da cutar annobar Ebola da kuma karfafa ayyyukan bunkasa fannin kula da lafiya. Yana mai cewa, Congo a shirye take ta yi aiki tare da Sin domin hada hannu wajen karfafa ci gaban dangantakar Sin da Afrika. (Suleiman Suleiman)



















