Nau’oin wuraren da za su iya ɗaukar jami’in ilimi aiki
Jami’an ilimi wuraren daban daban suke ɗaukarsu aiki kamar makarantun ilimi da suka hada da makaranta, Kwalejoji, da kuma Jami’oi da dai sauran makarantun ilimi.
Bugu da kari da akwai Hukumomin gwamnati da kuma Hukumomi wadanda ba domin riba aka kafa su ba, da kuma gidauniyoyi na ilimi suna iya hayar jami’an ilimi.
Su wadannan kwararrun sune suke da alhakin samarwa da gabatar tsare tsaren ilimi da kuma aiwatar da su, sai kuma iya tafiyar da manhajar siffofin koyarwa, ga kuma gabatar da manufofi,da sa ido wajen ganin yadda dalibi yake tafiyar da rayuwar karatun sa.Jami’an ilimi suna bada muhimmiyar gudunmawa wajen tabbatar da makarantun koyon ilimi suna samun nasara da kuma cewar su daliban suna karuwa da abubuwan da ake koya masu da ya sa ake da buƙatar jami’an ilimi.
- Cibiyar Ilimin Mata Ta Shirya Wa Sarakuna Da Malamai Taron Inganta Karatun Mata A Kaduna
- Uba Sani Ya Baiwa Wadanda Suka Lashe Musabakar Karatun Alkur’ani Kujerun Hajji
Ana matukar bukatar jami’an ilimi saboda kuwa sune suke da alhakin tabbatar dukkan tsare tsaren ilimi da manufofi ana amfani da su kamar yadda ya kamata.Suna aiki da Shugabannin makarantu da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da dalibai suna msaun nagartaccen ilimi.
Hakanan ma jami’an ilimi ma na bukatar su rika gabatar da horarwa ga Malamai da sauran ma’aikata kkan irin nau’oin dabarun na koyarwa da ba a dade da fara aiki da su ba.Ganin yadda ake ta kara maida hankali kan ilimi mai nagarta da kuma irin sauye sauyen da ke yawan samu ta bangaren ilimi,hakan shi yasa ake ta kara yawan bukatar jami’an ilimi shi yasa za a ci gaba da samun hakan a shekaru masu zuwa.
Abubuwan da ake bukata daga jami’in ilimi
Shi da jami’in ilimi abubuwan da ke bukatar ya mallaka saboda irin gudunmawar da yake badawa a ko wace rana wajen daukar mataki.Babban abinda ake bukata kowace rana ana tabbatar da kowa da kowa yana samun irin ilimi mai nagarta da ya dace ya samu,ba ta re da la’akari da cewar shi wanene ba,ya ya yake,mai arziki ne ko kuma shi wani tantirin matalauci ne, ko kuma wane irin tafarkin addini yake bi.
Jami’an ilimi dole ne su tabbatar da bi dukkan shharuddan ilimi kamar yadda ya kamata, ba tare da wada wata maganar da bata kamata a yada ta ba, wajen huldarsu, dalibai, iyalai, da kuma abokan aiki.Bayan haka ma duk abinda da za su yi wanda ya shafi daukar mataki abu mafi dacewa shi ne su yi hakan ta byadda abin zai taimakawa mai koyo, sai kuma tafiyar da lamarin ilimi da gaskiya, ba tare da nuna wani bambanci ba, duba yadda lamrin ilimi yake, da kuma hanyar bada rahoto.
Jami’an ilimi bu da ake fison gani suna yi shi ne su guji nuna duk wani abinda ya sabawa gaskiya babu kuma wani bambanci ba, a duk wata hanya ta gudanar da aikinsu.
Hanyar da mutum zai bi domin ya zama jami’in ilimi
Idan har mutum yana bukatar zama jami’in ilimi ya kamata ya samu mallakar satifiket din digiri kan lamarin daya shafi ilimi ko kuma wani abu mai nasaba da shi, wannan ya hada da ya kasance yana da kwarewa kan lamarin daya shafi koyarwa ma’ana ko ya taba aikin koyarwa a cikin aji.
Wasu jami’an ilimin ana da bukatar su samu mallaki takardar shedar ko lasin da yake nuna cewar da akwai wani sashe ko bangare na ilimi da suka kware ko maida hankalinsu akai.
Hakanan ma idan mutum ya sani kan kwarai yadda zai iya tafiyar da mu’amalar sa da mutane, da kuma yadda yake ba lamarin muhimmanci sosai, da kuma irin wayo na yadda zai iya yin aiki da sauran abokan aikinsa subna daga cikin abubuwan da ake bukata ya mallaka domin ya samu nasara kan aikinsa. Idan dai an mallaki karatun da samun ilimin da ake bukata da kuma kwarewa, sai kuma dabaru,wadanda suke bukatar a dauke su domin su zama jami’an ilim suna iya fara neman aikin ta fannin da ba za su taba yin dana- sani ba.
Wannan shi ne rubutu na karshe kan ayyukan jami’an ilimi da muhimmancinsu, inda kuma muka fara da halayen kirki 14 da ake bukatar Malamin makarnta ya kasance da su.
Haleyen Kirki 14 Da Ake Bukata Daga Wurin Malamin makaranta (1)
Idan ka fara yin tunani kan ilimin ka wanda ka samu na can baya ba za ka taba mantawa da wani Mlamai ba wanda ya zame maka wanda za ka rika tunawa da shi domin yana baka ko ya baka kwarin gwiwa,kana kuma koyi da yadda yake tafiyar da rayuwar aikinsa ta Malamin makaranta.
Me yiyuwa shi ko Farfesa ne wanda ya sa ka canza sauya irin aikin da ka ke son yi, ko kuma Malaminne wanda yake koyawa yara kananan wanda saboda irin halin kirkin shi ne ya sa ma ka samu sauyi a rayuwar ta yaro karami.Kai wannan ma duk ba wani abu bane duk dai wani kokarain da ka yi a wani darasin da ake koya maka, akwai wasu halaye abubuwan da ake bukatar Malamin makaranta ya Kasane yana da sun a dabarun da za su taimaka ma sa wadanda za ayi magana kan su a cikin wannan maudu’in, wadannan kamar yadda aka tsara bayyana su ,sune wasu alamun halayen kirki da ake bukatar ace Malamin makaranta ya mallake su ko ace yana da su.
Sai a ci gaba da karantawa yayin da kuma za a hadu da wasu halayen kirki 14 da ake son Malamin makaranta ace yana da su kamar yadda masana ilimi suke bukatar haka shekara 2032 har ma gaba da hakan.
Kai abin ma ha rya zarce haka domin kuwa har ma da irin nau’in takardun ilimin da ake bukata kafin wani ya cancanci zama Malamin makaranta.Ko dai kana bukatar ka kara samun dabaru ne na salon koyarwa ,yadda za a koyar ya kuma zama da’iman ne ka mallake su, ko kuma halaye ne ya kamata ace kana da irinsu, koma dai me nene ya dace ka yi, wadannan shawarwarin ko nau’oin halayen su ne ake bukatar su zama maka kamar wata manuniya ta yadda za ka rika bunkasa ilimin ka, saboda ta hakan ne za ka samu damar inganta takardar da ke bada bayanai na ko wanene kai ta bangaren ilimin da ka mallaka ko kake da shi.