ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, November 12, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ba A Kafa NBC Don Takura Wa Kafafen Yaɗa Labarai Ba – Minista Idris 

by Sulaiman
2 years ago
NBC

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talbijin ta Ƙasa (NBC) da ta rungumi masu harkar yaɗa labarai domin a binciki dokokin karya ƙa’idojin yaɗa labarai.

Ministan ya yi wannan kira ne a lokacin da ya kai ziyarar yini ɗaya a hedikwatar hukumar a Abuja.

  • Tinubu Ya Nada Olukoyede A Matsayin Sabon Shugaban EFCC
  • Kungiya Ta Yi Allah Wadai Da Wallafa Hoton Gwamna Uba Sani A Cece-ku-cen Rabon Mukaman Siyasa

Ya ce akwai buƙatar a sake saisaita alƙiblar hukumar ta yadda za a daina yi mata mummunar fassarar cewa ba ta da wani aiki ko amfani sai ƙaƙaba takunkumi, cin kafafen yaɗa labarai tara ko garƙame su.

ADVERTISEMENT

Ya ce: “Ni ban yi amanna da cewa NBC ba ta da wani aiki sai cin tarar kafafen yaɗa labarai ba. Saboda a duk lokacin da ka ji an yi maganar NBC a labarai, ba za ka ji komai ba sai batun wani gidan talbijin ko gidan rediyo ya karya doka.

“Amma ni ina ganin cewa ba a nan ya kamata a tsaya ba. Akwai buƙatar a wayar wa jama’a da kai sosai. A kan haka, ina ganin ba a taɓuka wani ƙoƙari wajen isar da saƙo ga jama’a.

LABARAI MASU NASABA

An Kama Direban Gwamnati Da Hannu A Satar Motar Ofishin Mataimakin Gwamnan Kano

Za Mu Kare Sojojin Da Ke Bakin Aiki — Ministan Tsaro

“Wajibi ne ku ƙara azama sosai, ta yadda mutane za su gane ku, kuma su fahimci irin ayyukan da su ka rataya a wuyan NBC, ba don komai ba sai saboda mutane ba su san waɗansu ayyukan NBC ba sai ƙaƙaba takunkumi, cin tara da garƙame kafafen yaɗa labarai.

“Ya kamata NBC ta himmatu wajen wayar da kan jama’a ta yadda za su fahimci cewa hukumar na da kyawawan tsare-tsaren ingantawa da bunƙasa fannonin watsa labarai. Ba ƙaƙaba takunkumi ko ladabtarwa kaɗai ne aikin hukumar ba.

“Ina sane da cewa ku na ƙoƙari sosai, amma akwai buƙatar ku ƙara ƙaimi a waɗannan batutuwa domin sai fa idan kun yi haka ne ‘yan Nijeriya za su daina kallon cewa ba ku da wani tasiri sai hukunta kafafen da su ka karya doka kawai. Ku tashi ku nuna ku abokan haɗa hannu da ƙarfi ne domin kawo ci gaba.”

Ministan ya ƙara da cewa ƙoƙarin da ake yi yanzu haka a Majalisar Tarayya don yi wa Dokar NBC garambawul abu ne mai kyau.

Ya ce, “Saboda lokacin da aka kafa NBC, ba a yi la’akari da wasu muhimman batutuwa ba, dalili kenan buƙatar yi wa dokar garambawul ta taso.”

Idris, wanda shi ne Kaakaki Nupe, ya nuna gamsuwar sa ganin irin hoɓɓasan da NBC ta yi a shirye-shiryen ɗaukar nauyin taron AFRICAST da za a yi a cikin wannan wata.

Da ya ke bayani ga ministan, Babban Daraktan NBC, Malam Balarabe Shehu Ilelah, ya ce hukumar na da rassa 28 a cikin jihohi daban-daban, sai Ofisoshin Shiyya guda goma, sannan kuma ta na da ma’aikata 419.

Ya ce NBC ta na sa ido kan tashoshi 777, waɗanda a cikin su akwai gidajen rediyo 609 da tashoshin talbijin 168.

Ya ce, “Yayin da mu ke aikin sa-ido, mun bada gargaɗi sau 3,312 a 2022 da 2023. Cikin 2022 kuma an hukunta tashoshi 125.

“Mun aika da gargaɗi sau 1,238 a cikin 2023, sannan kuma an ladabtar da tashoshi 62.”

Ilelah ya shaida wa ministan cewa NBC na bin gidajen rediyo da tashoshin talbijin bashin da ya haura naira biliyan uku.

Ya ce dalili kenan ma a cikin Mayu 2022, hukumar ta buga sunayen dukkan waɗanda ta ke bi basussukan a cikin jaridun ƙasar nan.

Ya ce, “Daga lokacin ne mu ka ba su wa’adin su canja lasisin su tare da biyan basussuka, ko kuma a soke lasisin baki ɗaya.

“An samu tashoshi 52 da ba su biya ba, watanni uku bayan cikar wa’adi. Hakan ne ya sa NBC ta yi amfani da doka, ta soke lasisin su a ranar 19 ga Agusta, 2022.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa
Manyan Labarai

An Kama Direban Gwamnati Da Hannu A Satar Motar Ofishin Mataimakin Gwamnan Kano

November 12, 2025
Za Mu Kare Sojojin Da Ke Bakin Aiki — Ministan Tsaro
Manyan Labarai

Za Mu Kare Sojojin Da Ke Bakin Aiki — Ministan Tsaro

November 12, 2025
‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 3 Tare Da Sace Babur A Nasarawa
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 3 Tare Da Sace Babur A Nasarawa

November 12, 2025
Next Post
‘Yan Bindiga Sun Kashe Dan Agaji Bayan Da Ya Kai Musu Kudin Fansa A Kaduna

‘Yan Bindiga Sun Kashe Dan Agaji Bayan Da Ya Kai Musu Kudin Fansa A Kaduna

LABARAI MASU NASABA

Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

An Kama Direban Gwamnati Da Hannu A Satar Motar Ofishin Mataimakin Gwamnan Kano

November 12, 2025
Sin Ta Yi Kira Da A Inganta Mika Mulki Cikin Kwanciyar Hankali A Sudan Ta Kudu

Sin Ta Yi Kira Da A Inganta Mika Mulki Cikin Kwanciyar Hankali A Sudan Ta Kudu

November 12, 2025
Za Mu Kare Sojojin Da Ke Bakin Aiki — Ministan Tsaro

Za Mu Kare Sojojin Da Ke Bakin Aiki — Ministan Tsaro

November 12, 2025
‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 3 Tare Da Sace Babur A Nasarawa

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 3 Tare Da Sace Babur A Nasarawa

November 12, 2025
‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi Sama Da 200 A Katsina

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi Sama Da 200 A Katsina

November 12, 2025
Injiniya Sagir Ibrahim Ƙoƙi Ya Fice Daga Jam’iyyar NNPP

Injiniya Sagir Ibrahim Ƙoƙi Ya Fice Daga Jam’iyyar NNPP

November 12, 2025
Bayanan Da Muka Samu Sun Nuna An Fara Samun Tsaro A Nijeriya – Hafsan Sojin Ƙasa

Bayanan Da Muka Samu Sun Nuna An Fara Samun Tsaro A Nijeriya – Hafsan Sojin Ƙasa

November 12, 2025
Yadda Ɓarawo Ya Shiga Gidan Gwamnatin Kano Ya Saci Motar Ayarin Mataimakin Gwamna

Yadda Ɓarawo Ya Shiga Gidan Gwamnatin Kano Ya Saci Motar Ayarin Mataimakin Gwamna

November 12, 2025
Zargin Kisan Kiristoci: Dalilan Da Ya Sa Trump Ba Zai Iya Kai Wa Nijeriya Hari Ba

Zargin Kisan Kiristoci: Dalilan Da Ya Sa Trump Ba Zai Iya Kai Wa Nijeriya Hari Ba

November 12, 2025
Coas

Bayan Ganawa Da Tinubu, COAS Ya Tabbatar Wa ‘Yan Nijeriya Samun Ingantaccen Tsaro

November 11, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.