A wannan mako ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya fadawa shugaban masu rinjaye na majalisar dattawan kasar Amurka Chuck Schumer, wanda ya jagoranci wata tawagar ’yan majalisar dokokin Amurka don kawo ziyara kasar Sin cewa, a wannan duniya mai cike da sauye-sauye da rudani, yadda kasashen Sin da Amurka za su daidaita, shi ne zai iya tabbatar da makomar bil Adama.
Shugaba Xi ya ce, a matsayinsu na manyan kasashe biyu, ya kamata Sin da Amurka su nuna himma, da hangen nesa, da kaiwa ga matsayin da kasashen duniya ke fata, da kokarin inganta jin dadin jama’arsu, da ingiza ci gaban bil Adama.
- Sakamako Da Aka Samu Bayan Gina Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya
- Daliban Cibiyar Koyar Da Ilmin Sana’a Ta Luban Dake Djibouti
Bugu da kari, yayin da duniya da ma zamani ke sauyawa, har yanzu tunanin tarihi na zaman lafiya tsakanin kasashen Sin da Amurka bai sauya ba, haka kuma babban burin jama’arsu na yin mu’amala da yin hadin gwiwa bai canja ba, kana fatan da kasashen duniya ke yi na samun kwanciyar hankali da bunkasuwar dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka bai sauya ba.
Ya kuma bukaci bangarorin biyu da su mutunta juna, su zauna tare cikin lumana, da yin hadin gwiwa domin samun nasara tare. Manufar kasashen 2 dai ita ce, su daidaita da kuma kyautata alakarsu, da samar da hanyar da ta dace don yin cudanya da juna a sabon zamani na tarihi.
A nasa bangare Schumer ya gabatar da ra’ayoyin da suka dace na bangaren Amurka, ya kuma bayyana aniyar karfafa tuntuba da tattaunawa da kasar Sin bisa gaskiya da mutunta juna, da kuma lura da bambance-bambance dake tsakaninsu bil hakki da gaskiya da kaucewa tayar da rikice-rikice, kuma Amurka ba za ta raba gari da Sin ba.
Haka ma yayin ziyarar da sakatariyar baitul malin Amurka Janet Yellen ta kawo kasar Sin ta bayyana aniyarta ta kara yaukaka alaka, da cudanya da hadin gwiwa, da mutunta juna tsakanin kasashen biyu. Amma da komarwa Amurka sai aka ji ta tana furta wasu manufofin Amurka da ba su dace ba kan kasar Sin., ta hanyar fakewa da batun tsaron kasa.
Wannan dai ba shi ne karon farko da ake jin kasashen biyu na furta irin wadannan kalamai ba, amma daga karshe sai a wayi gari Amurka ta sa kafa ta yi fatali da abin da ta furta ko aka cimma, matakin dake sake mayar da hannun agogon baya a hadin gwiwar kasashen dake zama mafiya karfin tattalin arziki a duniya.
Idan ba a manta ba, ko shi ma sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken yayin da ya kawo makamanciyar wannan ziyara kasar Sin a wannan shekara, ya furta irin wadannan kalamai na karfafa alaka da mutunta alkawuran da aka cimma, amma bayan komawarsa gida, sai aka ji shi yana furta wasu kalamai marasa dacewa game da alakar sassan biyu.
Masu fashin baki dai na cewa, ya dace Amurka ta rika nuna sanin ya kamata ta kuma cika alkawuran da ta yi, tare da daina neman bata sunan kasar Sin ko kakaba mata takunkuman da ko kadan ba su dace ba. Don haka, a wannan karon ma, ba za a yi saurin gaskata kalaman jagoran tawagar ’yan majalisun dokokin na Amurka ba. Masu iya magana na cewa, ba a yabon dan kuturu, sai ya shekara da dan yatsa.
Duniya dai ta zuba ido tare da fatan gwamnatin Amurka, za ta dauki hakikanin matakai domin ciyar da huldarta da Sin gaba yadda ya kamata, wadda ke da muhimmanci ba ma ga kasashen biyu ba, har ma ga duniya baki daya. (Ibrahim Yaya)