Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Dakta Chris Ngige, ya caccaki tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo kan sukar shugaban kasa, Muhammadu Buhari a cikin wasikar sabuwar shekara da ya rubuta wa ‘yan Nijeriya.
Tsohon gwamnan jihar Anambra ya ce manyan ‘yan takarar shugaban kasa guda hudu dukkansu suna da kyakkyawar manufa da sanin makamar tafiyar da al’amuran kasar, don haka babu wanda zai taya yakin neman zabe daga cikinsu.
Ngige, wanda ya zanta da manema labarai a mahaifarsa ta Alor, karamar hukumar Idemili ta kudu a jihar Anambra a ranar Laraba, ya ce manyan ‘yan takarar shugaban kasar su ne Alhaji Abubakar Atiku, jam’iyyar PDP; Asiwaju Bola Tinubu, jam’iyyar APC mai mulki; Peter. Obi, jam’iyyar Labour (LP), da Alhaji Rabi’u Kwankwaso na jam’iyyar NNPP.
Ngige ya shaidawa dimbin jama’ar da suka taru a harabar cocin St. Mary’s Pavilion da ke Alor cewa, gwamnatin tarayya ta san mawuyacin halin da jama’a ke ciki, sabida haka ne gwamnatin ta bukaci ministoci su koma gida domin taimakawa mutanensu tun a watan Satumba.
Ya yi ikirarin cewa bai kamata a zargi gwamnati mai ci da matsalar yunwa da karancin mai ba da ake fama da ita a kasar nan, domin duk duniya ana fama da irin matsalar, ba wai a Nijeriya kadai ba.
Ngige ya kuma caccaki ikirarin Obasanjo na cewa Nijeriya ta koma baya inda ta ke a farkon shugabancinsa a shekarar 1999.