Shugaban rundunar adalci ta Jihar Sakkwato, Basharu Altine Guyawa Isa ya bayyana cewa gawurtaccen jagoran ‘yan ta’adda da ke hana wa al’umma bacci da idanu biyu, Bello Turji bai aminta da matakin sulhu da kowa ba.
Guyawa, wanda ya yi fice wajen fallasa ciki da wajen ayyukan ta’addanci a gabashin Sakkwato da Zam-fara ya bayyana cewa Æ™arfin bindiga kawai zai sa Turji ya ajiye makamai amma ba ta hanyar sulhu ba.
- Bello Turji Bai Yi Sulhu Da Kowa Ba – Guyawa Isa
- Askarawan Zamfara Sun Kashe Riƙaƙƙen Ɗan Bindiga, Kacalla Ɗanbokolo Ubangidan Turji
Ya ce, “Ƙasarmu guda, yankinmu guda, gidanmu guda da Bello Turji don haka muna sane da duk abin da yake yi, idan ya ajiye makamai, to wa ya baiwa kuma kan wani sharaÉ—i ya ajiye makamai?,” in ji shi.
Guyawa ya bayyana cewa Sheikh Musa Assadus- Sunna da ya ce Turji ya ajiye makamai ba gaskiya ba ne, ya dai ga É—an bindigan kuma ya ba da labarin ganin sa, ya ce idan har Sheikh Ahmad Gummi da yake babban malami mai kima da martaba zai kasa jagorantar sulhun, to shi ma ba zai iya ba.
Matashin wanda ya É—auki shekaru yana fafatukar ganin an kawo Æ™arshen matsalolin tsaro a gabascin Sakkwato tare da bai wa jami’an tsaro bayanan sirri, ya ce ba a taÉ“a yin sulhu kuma a ci gaba da cin zarafin jama’a ba.
“Shin an taÉ“a yin sulhu a na cin zarafin jama’a, an taÉ“a yin sulhu a na sa manoma noman dole, an taÉ“a yin sulhu a na karbar harajin dole, an taÉ“a yin sulhu ba a ajiye makamai ba?”
Ya ce Turji da sauran ‘yan bindigansa irin su Kachalla Choma da Kachalla Haru ba za su ajiye makami ba, ya ce suna da kwamandoji da makaman da sun fi a kirga.
Guyawa ya bayyana cewa Malamin bai san Turji ba, bai kuma san yankinsu ba, ya ce su da suke a yankin sun tabbatar Turji bai ajiye makami ba, kuma bai yi sulhu da kowa ba.
Ya ce a kwanan baya Turji ya kashe jami’an tsaro tare da Æ™one motarsu, don haka idan ya yi sulhu ba zai yi hakan ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp