Da alamu siyasar Jihar Kaduna ta ɗauki sabon salo bayan ɗan tsohon gwamnan jihar, Bashir El-Rufa’i ya caccaki gwamnan jihar, Uba Sani da cewa ba ya taɓuka wa jihar komai face yin barci a Abuja.
Bashir ya yi waɗannan kalaman ne a lokacin da yake yi wa Uba Sani raddi l, bayan ya bayyana cewar gwamnatin El-Rufa’i ba abin da ta bar wa jihar face ɗimbin bashi.
- El-Rufai Ya Jibge Min Bashin $587 Da Biliyan 85 A Kaduna – Uba Sani
- Fyade: An Yanke Wa Robinho Zaman Gidan Kaso Na Shekara Tara
Leadership Hausa ta ruwaito yadda Gwamnan Kaduna, Uba Sani ya kwancewa tsohuwar gwamnatin Nasiru El-Rufa’i zani a wani taro da ya gudana a jihar.
Ya yi ikirarin cewa tsohuwar gwamnatin ta bar musu bashin dala miliyan 587 da bashi Naira biliyan 85, wanda hakan ya sa jihar ba ta iya biyan ma’aikata albashi.
Waɗannan kalaman gwamnan jihar, sun sanya Bashir yi wa Uba Sani kakkausar suka a shafinsa na X, inda ya ce kamata ya yi gwamnan ya mayar da hankali wajen gudanar da gwamnatinsa a jihar maimakon ɗora wa gwamnatin El-Rufa’i laifi kan halin da jihar ke ciki.
Ya ƙara da cewa Gwamna Uba Sani tare da muƙarrabansa ba su da wani aikin da ya wuce zuwa Abuja yin barci da shiririta.
Ya ce “Sun gano cewa ba wani abu da za su iya yi wa Jihar Kaduna a gwamnatance, face gwamnan da tawagarsa zuwa Abuja yin barci da yin abubuwa marasa amfani”.
Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani da tsohon gwamnan Jihar Nasir El-Rufa’i dai aminan juna ne, kuma El-Rufa’i ne ya goya masa baya har ya samu tikitin takarar jam’iyyar APC, da ya kai shi ga nasara a zaben 2023