Za a iya alakanta kokarin da Gwamnatin Tarayya mai ci ke kan yi, wajen gasar bunaka tattalin azriki da kuma inganta rayuwar ‘yan Nijeriya duba da cewa sun kasance, suna ci gaba da fuskantar matsin tattalin arziki da kuma ci gaba da fuskantar kalubalen rashin tsaro.
A yayin bude taron yaki da safararar haramtattun kudade da dakile biyan kudaden daukar nauyin ta’addanci tare da kuma yakar bazuwar kanannan makamai a hannun jama’a da aka gudanar a Abuja na 2025, Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya shedawa mahalarta taron cewa, Gwamnatinsa daidai da dabaraun dakile yakar ta’addanci, ta kasa wato NCTFS, ta karfafa karfinta tare da kuma ci gaba da zakulo masu daukar nauyin ta’addanci a kasar.
- Sojoji Sun Tarwatsa Sansanin Lakurawa A Sokoto Da Kebbi, Tare Da Ƙwato Makamai
- Babu Sauran Burbushin ‘Yan Ta’addan Lakurawa A Arewa Maso Yamma – Ministan Tsaro
Tinubu, ya sanar da hakan ne, ta bakin Sakataren Gwamnatin Tarayya Sanata George Akume, inda ya sanar da cewa, ta hanyar kokarin da ofishin Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara ta Musamman a Fannin Tsaro da kuma kokarin Akanta Janar kuma Ministan Shari’a ke yi, Gwamnatin Tarayya, a cikin shekaru biyu, ta samu nasarar gurfanarwa a gaban Kotu da kuma yankewa irin wadannan mutanen da ke daukar nauyin ta’adanci sama da 100 hukunci.
Mu a wannan Jaridar, muna jinjinawa Gwamnatin Tarayya, kan wannna nasarar, tare da kuma ba ta shawarar cewa, da ta kara kaimi, wajen yaki da duk wani na’ui na aikata manyan laifuka, musamman ayyukan ta’addanci, fashin Daji, garkuwa da mutane, tayar da kayar baya da kuma tayar da tashin tashina, a daukacin fadin Nijeriya, musamman duba da cewa, wa’adannan ayyukan, sun kai ga durkusar da kasar da kuma ‘yan kasar, biyo bayan vullar ta’addaci da kuma bayyanar masu hakilon a raba Nijeriya gida biyu.
Sai dai, wani hanzari ba gudu ba, bama goyon bayan yiwa masu daukar nauyin aikata ayyukan ta’addanci da kuma ‘yan ta’addar, Shari’a a, asirce.
Hujjar mu a nan ita ce, kundin tsarin mulkin Nijeriya, sama yake da kowanne dan kasar da kuma sauran dokokin kasar, duba da cewa, kundin ya bayar da damar a yi Shari’ar a bisa adalci kuma a bayyane, ga wadanda ake tuhumar da aikata laifi.
Bugu da kari, dole ne mu tuhumi matakan da mahukuntan kasar suka dauka na yiwa wadanda ake tuhumar Shari’ar a, asirce.
Akwai dimbin tambayoyi a zukatan ‘yan Nijeriya wanda kuma suke bukatar amsa, misali, a ina ne aka cafke su? ta yaya ne, aka kama su? yaushe ne, aka gurfanar da su, a gaban Kotu? Shin an barsu sun dauki Lauyoyin da za su tsaya masu gaban Kotu? har tsawon wanne lokaci ne, suke ci gaba da fuskantar Shari’a kuma kan wanne laifi ne, Kotu ke tuhumarsu?, me ya sanya ake yi masu Sharia’a a, asirce?
Tabbas, ‘yan Nijeriya na bukatar amsar wadannan tambayoyin, duba da cewa, kamata ya yi, a ce, ana yin masu Shari’ar bisa bin ka’ida, ko dai mutum dan kasa ne ko kuma bakin haure ne, ya kamata a ce, ana yi masu Shari’ar a bayya ne.
Yi wa mutanen, Shari’ar a, asirce ya savawa ka’ida duba da cewa, kundin tsarin mulkin Nijeriya, ya tanadi a bai wa, duk wanda ake zargi, ‘yancin da yi masa adalaci, kan tuhumar da ake yi masa.
Wannan Shari’ar da ake yiwa mutanen a asirce, hakan ya jefa ‘yan Nijeriya a cikin bakin duhun, sanin hakikanin yadda Shari’ar ke tafiya, hujojin da aka gabatar a kansu a gaban Kotu tare da kuma cewar, wadanda Kotun ke tuhuma, a kan wanne takamaiman laifi ne, aka gurnar da su kuma wanne irin hukuncin da aka yanke masu.
Hakan ya nuna cewa, rashin bin ka’ida a yi masu Shari’ar, tare da taka dokar kasa da kuma take ‘yancin ‘yan Adam.
Kazalika, hakan ya sanya nuna rashin aminta da Gwamnatin Tarayya, na cewa, ko za yi hukuncin bisa gaskiya.
Abin tambaya a nan shi ne, ta yaya irin wadannan gungun tantiran ‘yan ta’addar, musamman ‘yan ta’addar Boko Haram da suka fara aikita ta’addancin su tun a 2009, a kuma ce wai za yi masu Shari’a asirce?
‘Yan Nijeriya na bukatar sanin shi wadanne mutane ne, ke taimakawa ‘yan ta’addar wajen aikata ta’asarsu.
A gafe daya kuma, ‘yan ta’addar na ci gaba da kai farmaki ga sansanonin dakarun soji tare da kuma hallaka su da kuma kashe sauran fararne Hula, ciki har da dattijai, mata da kuma yara, inda ta’asar ta su, ta mayar da yaran marayu, matan kuma suka zama zawarawa ba tare da sun aikatawa ‘yan ta’addar wani laifi ba.
‘Yan ta’addar, sun zama tamkar, wasu mala’ikun mutuwa sanadiyyar kisan da suke yi, hakan ya janyo tarwatsa mafarkin wadanda lamarin ya rutsa da su da kuma tarwatsa su, daga matsugunan su, da suka gada tun daga kaka da kakanni.
Har zuwa yau, ‘yan makarantar Boko, musamman ‘ya’ya mata ana ci gaba da yin garkuwa da su, a wasu sassan kasar nan, tare da kuma yadda ‘yan ta’addar ke tilasta su, su aure su da kuma sanya su a aikin bauta.
‘Yan Nijeriya na ci gaba da hadiye fishinsu duba da cewa, wadanda suka dauki nau’yin ‘yan ta’addar da suka aikata masu ta’asar, amma Gwamnatin Tarayya ta yi uwa ta kuma yi makarviya, wajen kin yiwa ‘yan ta’addar da masu daukar nauyinsu Shari’a a asirce.
A namu ra’ayin domin ‘yan Nijeriya su yi ammana da Shari’ar da ake yiwa wadnda ake tuhumar a, asirce, ya zama wajbi Gwamnatin Tarayaya ta bayyana su, ta hanyar wallafa sunayensu, hotunansu, kanannan hukumomin da suka fito da kuma jihohin su na haihuwa, irin laifin da suka aikata aka kaisu gidan kaso da kuma irin hukuncin da aka yanke masu, a cikin a Jaridun kasar.
Yin hakan zai bai wa kamfanoni masu zaman kansu yanke duk wata nau’in hada-hadar kasuwanci da su da kuma hana hukumomin gwamnati daukar su, aiki.
Muna shawartar Gwamnatin Tarayya cewa, da ta sake yin tunani, kan dabarun da ta dauka, na yiwa wadnada ake tuhumar, Shari’ar asirce.
Daukar wannan shawarar na da matukar mahimmanci, musamman domin a tabbatar da yin gaskiya da adalci tare da kuma kare kimar ‘yancin Adam da kuma girmama dokar kasa.
Hakazalika, Gwamnatin Tarayya, ta tabbatar da yi masu Sharia’r bisa gaskiya, a bar su, su dauki Lauyoyi da za su tsaya masu, kuma hujjojin da aka gabatar kan zarginsu, su kasance na gaskiya ne, wadanda kuma za a iya gabatarwa, a gaban Kotu.
Abu ne, mai kyau a yaki da ta’addanci, amma ya kamata a yi hakan, ta hanyar mutunta ‘yancin daidaikun mutane, tabbatar da yin gaskiya da adalci da kuma mutunta, ‘yancin ‘yan Adam.
Batun yi wa masu aikata ta’addanci Shari’a ko kuma masu daukar nauyin aikata ta’addanci a kasar nan a, asirce, abu ne da ya savawa turbar mulkin Dimokiradayyar Nijeriya.