Gwamnatin Tarayya ta mayar da martani kan kalaman Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, kan tsare-tsaren gyaran tattalin arziki da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu take aiwatarwa, tana mai bayyana su a matsayin marasa amfani kuma na son rai.
A wata sanarwa da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya fitar a ranar Laraba, ya bayyana cewa Nijeriya tana cikin wani muhimmin mataki da ke buƙatar matakan da suka dace da kuma ƙarfin hali domin magance manyan matsalolin tattalin arziki.
- Bukatar Sanin Hakikanin Halin Da Tattalin Arzikin Nijeriya Ke Ciki
- Jarumin Bollywood Saif Ali Khan Ya Tsallake Rijiya Da Baya
Ministan ya nuna jin daɗin sa kan yadda Sanusi ya amince da wasu tsare-tsaren gwamnati, amma ya nuna damuwa kan yadda Sarkin ya bayyana cewa ba zai goyi bayan gwamnati ba saboda wasu dalilai na son rai.
Ya ce: “Abin takaici ne yadda shugaba daga masarauta mai daraja da son tsare gaskiya da adalci zai fito fili ya ce ba zai faɗi gaskiya ba saboda dalilan kan sa.”
Ya jaddada cewa gyare-gyaren da gwamnatin ta yi, kamar daidaita farashin dala da kuma cire tallafin man fetur, sun zama dole domin magance shekaru na gazawa wajen gudanar da tattalin arzikin ƙasa.
Idris ya bayyana cewa an fara ganin sakamakon waɗannan matakai ƙarara, wanda ya haɗa da ƙaruwar ajiyar kuɗaɗen waje, ƙaruwar ƙwarin gwiwar masu zuba hannun jari, da rage yawan bashin da ake biya.
Ministan ya bayyana cewa sukar da sarkin ya yi ba ta dace ba, musamman ganin cewa ya taɓa goyon bayan irin waɗannan matakan a baya. Ya yi kira ga Sanusi da ya fifita cigaban ƙasa a kan son rai.
Ya ce: “Gyaran Nijeriya tana buƙatar haɗin kai, mayar da hankali, da sadaukarwa daga dukkan masu ruwa da tsaki.
“Ya kamata shugabanni su zama jagororin cimma muradun cigaban ƙasa, ba masu tauye amanar jama’a ba.”
Idris ya sake tabbatar da aniyar gwamnatin ta bunƙasa tattalin arziki mai ɗorewa, tare da yin kira ga ’yan Nijeriya su ba da haɗin kai domin samun nasarar waɗannan tsare-tsare.
Ministan ya jaddada cewa gwamnati a shirye take don tattaunawa mai amfani da dukkan masu ruwa da tsaki, tare da tabbatar da cewa tana kan hanyar cika burin samar da ƙasa mai inganci ga kowa.