Kwamishinan matasa da wasanni na jihar Bauchi ya shaida cewar hotuna mai motsi da ake yadawa da ke nuna wani mutum na mika wa mata kudi da bukatar su zabi PDP, ya ce sam ba shi ba ne.
Kwamishinan a hirarsa da wakilin gidan rediyon VOA Hausa, ya nuna damuwarsa kan hoton aka yada da aka danganta da shi, ya yi barazanar daukan matakin shari’a.
Wakilinmu ya labarto cewa tun jiya Juma’a ne dai wani bidiyo ya yi ya yawo a duniya inda ake cewa wani kwamishina a jihar Bauchi ya rabon kudi don a zabi PDP. Bidiyon ya yi yawo sosai a shafukan Tweeter.
A cewarsa, “Sunana Honorable Adamu Manu Soro kwamishina na matasa da wasanni na jihar Bauchi.
“Wannan hoton bidiyon da ake yadawa tazuniya ce duk wanda ya San jihar Bauchi ya San Mai girma gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad (Kauran Bauchi) ya yi kokari a wajen ayyuka a gani da a tabbatar, don haka ba sai wani jami’insa ya je yana sayen kuri’a ba. Al’ummar jihar Bauchi sun san Kaura ya yi kuma sun gani a kasa.
“Sam ba nine a wannan hoton ba kuma na yi hira da wata kayar yada labarai na gaya musu cewa wannan hotun ha nina ba ne, Kuma duk wata jarida ko mutumin da ya wallafa wannan labarin ya yi ne domin ya bata min suna Kuma insha Allahu ni zan nemi hakkina ta bangaren shari’a”