Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya yi zargin wasu miyagun mutane na daukar nauyin wasu matasa da nufin tayar da tarzoma da haifar da rashin zaman lafiya a jihar.
Gwamna Fintiri ya ce ingantattun bayanan sirri game da ayyukan wasu matasa da ke shirin kutsawa cikin rumbunan gwamnati da na masu zaman kansu, da nufin su fasa, ya ce gwamnatinsa za ta yi maganin duk wanda ke barazana ga zaman lafiyar jihar, domin bukatar kashin kai.
- ‘Yan Kasuwar Singa A Kano Sun Musanta Zarge-zargen Ɓoye Kayan Abinci
- Tsare-tsaren Da Buhari Ya Kawo Ne Suka Janyo Halin Da Nijeriya Ke Ciki – Oshiomhole
Cikin wata sanarwar manema labarai da jami’in yada labaran gwamnan, Humwashi Wonosikou, ya rabawa manema labarai, ta ce, “Gwamnati ba za ta tsaya tana kallon ‘yan tada zaune da masu daukar nauyinsu suna ingiza jama’a su dauki doka a hannunsu ba.
“Ba zan nade hannuna in kalli wani ko wata kungiyar mutane da ke kokarin yi wa gwamnati zagon kasa ba.” inji sanarwar gwamnan
Sanarwar ta ce gwamna Fintiri ya yi mamakin dalilin da ya sa mutanen ke kin yin amfani da hanyoyin da doka ta tanada don magance matsalolinsu, maimakon haka suna shirin yin zagon kasa ga zaman lafiyar jihar.
“Muna sane da cewa wasu a cikin al’ummarmu suna baiwa wadannan ‘yan ta’adda goyon baya don ganin sun kawo cikas ga zaman lafiya a jiharmu, ina mai tabbatar musu ba za su yi nasara ba, za mu tabbatar da cewa ba su yi nasara ba” sanarwar ta jaddada.