Hukumar zabe ta kasa ta ce ba za a yi zabe a cibiyoyi kusan 240 ba a jihohi 28 a kasar lokacin zabukan da ke tafe, ranar 25 ga Fabarairu da kuma 11 ga watan Maris.
BBC Hausa ta rawaito cewa, Shugaban hukumar, INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a yau Litinin lokacin da yake ganawar da ya saba da shugabannin jam’iyyu 18 masu rijista, a Abuja.
- Mun Shirya Wa Masu Fizgen Na’urar Tantance Rajistar Zaɓe – INEC
- 2023: Kashi 90 Na Shirye-Shiryen Zabe Ya Kammala – INEC
Shugaban ya ce dalilin hakan kuwa shi ne babu wani mai zabe da ya yi rijista a wadannan cibiyoyi 240.
Ya ce cibiyoyin da ba za a yi zaben ba suna jihohin Zamfara da Kwara da Edo da Rivers da kuma Imo wadda tafi yawansu da 38.
Farfesan ya ce bayan cibiyoyin 240 da ba za a yi zaben ba, duka sauran cibiyoyi kusan 176,606 a fadin kasar za a yi zabe.
Hukumar ta kuma yi gargadin cewa ba za ta amince da yanayin da jam’iyya daya za ta tura wakili fiye da daya ba a cibiyar zabe, su haddasa rudani ba, tana mai cewa duk wakilin da aka samu yana haka za a kama shi a gurfanar da shi gaban shari’a.