Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad, ya naɗa babban yayansa, Alhaji Adamu Muhammad Duguri, a matsayin Sarkin Duguri, Sarki mai daraja ta ɗaya, a sabuwar masarautar Duguri.
A lokacin da ya karɓi wasiƙar naɗinsa daga tawagar gwamnatin jihar a ranar Juma’a, sabon Sarkin Duguri ya ce zai yi aiki tare da sauran sarakunan Jihar Bauchi domin kawo ci gaba.
- Gwamnatin Kaduna Ta Gano Ma’adanin Zinari Da Tagulla Da Za Su Haɓaka Tattalin Arziƙin Jihar
- Shugaban Kasar Sin Zai Halarci Taron APEC Da Ziyarar Aiki A Korea Ta Kudu
Ya bayyana cewa zai girmama manyan sarakuna, musamman Sarkin Bauchi, Dakta Rilwanu Sulaiman Adamu, tare da yin biyayya da mutunta su domin tabbatar da zaman lafiya da jagoranci na gaskiya.
Sarkin ya ce: “Zan yi aiki da manyan sarakuna cikin mutunci da biyayya. Ba zan jawo fitina ko rikici ba. Za mu yi aiki tare domin zaman lafiya da ci gaban kowa.”
Alhaji Adamu, wanda tsohon jami’in Kwastam ne da ya yi ritaya a matsayin mataimakin Kwanturola, ya ce zai yi aiki da gwamnati da bin doka domin inganta rayuwar jama’a.
Ya bayyana cewa sarakuna suna taka muhimmiyar rawa wajen kawo ci gaba, musamman a fannin ilimi, inda ya ce zai tabbatar yara sun koma makaranta.
Haka kuma, ya ce zai goyi bayan gwamnati a ɓangaren kiwon lafiya da tsaro, domin inganta rayuwar jama’a.
Sabon Sarkin, wanda kuma shi ne shugaban hukumar kula da ilimi a matakin farko (SUBEB) ta Jihar Bauchi, ya bayyana farin cikinsa da godiyarsa ga Allah da Gwamna Bala Muhammad saboda wannan dama da ya samu.
Ya yi alƙawarin yin aiki tuƙuru domin ci gaban masarautarsa da Jihar Bauchi gaba ɗaya, tare da kira ga jama’ar Duguri da su haɗa kai wajen gina masarautar.
“Mu mutanen Duguri a shirye muke mu taimaka wa gwamnati a duk abin da ta ce. Za mu tura yara makaranta, za mu karɓi rigakafi, kuma za mu ci gaba da zaman lafiya da maƙwabtanmu. Muna godiya sosai ga Gwamna Bala Muhammad bisa wannan dama,” in ji Sarki Adamu.
Sarkin ya bai wa Gwamnan Bauchi sarautar ‘Yariman Duguri.
Da yake miƙa takardar naɗin sarautar, Sakataren Gwamnatin Jihar Bauchi, Aminu Hammayo, ya ce Gwamna Bala Muhammad ya yi amfani da dokar masarautu ta shekarar 2025, musamman sashe na 16 da 17, wajen tabbatar da wannan naɗi.
Ya tunatar da sabon Sarki da ya tafiyar da harkokin masarautar bisa kundin tsarin mulkin ƙasa, dokokin Jihar Bauchi, da umarnin gwamnati, tare da tabbatar da adalci da gaskiya a shugabancinsa.
Gwamnan ya yi fatan sabon Sarkin zai jagoranci masarautar cikin zaman lafiya, haɗin kai, da samar wa al’ummar Duguri da Bauchi ci gaba.












