Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu ya bayyna babban dalilin da ya sa jam’iyyar APC ta fadi zaben gwamna a Jihar Kano.
Ya ce sace kai da wasu jiga-jigan APC ya janyo wa jam’iyyar shan kaye a zaben gwamna wanda har dan takarar NNPP, Abba Kabir Yusuf ya samu nasara da kuri’a 1,019,602, yayin da Nasir Yusuf Gawuna na APC ya samu kuri’u 890,705 a zaben gwamnan da aka kammala.
Sai dai a wata hira da sashen Hausa na BBC ya yi da shugaban jam’iyyar APC ya ce abin bakin ciki ne ga jam’iyyar mai mulki ta rasa muhimmiyar jiha kamar Kano, inda ya ce jam’iyyar za ta dauki mataki kan ‘ya’yanta da suka yi laifi.
Ya ce, “Laifin wasu ne ya sa muka yi rashin nasara a Kano. Akwai wadanda ba su yi abin da ya kamata ba.
“Kano na cikin jihohin da muke bugun kirji mu ce wannan namu ne, domin duk abin da za mu yi, Kano ce kan gaba a jerin sunayenmu.
“Amma saboda son kai, mun tsinci kanmu a cikin wannan hali. Bai kamata mu rasa Kano ba, amma duk abin da ya faru da mutum, Allah ne ya kaddara.
“Mun gargadi dukkan gwamnonin APC a Nijeriya da su kawar da duk wani nau’in son kai kafin zabe, kuma muna tunanin son kai ne ya kai mu ga rashin nasara a jiha kamar Kano.”