Babban hafsan sojojin kasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, ya nanata cewa rundunar sojin Nijeriya ba ta da wani shiri na tumbuke dimokuradiyyar a kasar nan.
Ya ce tsarin dimokuradiyya ya kafu da kafafunsa kuma za a ci gaba da shi wajen gudanar da ayyukan raya kasa wanda ‘yan kasa ke amfana, amma rashin sani ya sa wasu daga cikin ‘yan kasa ke kiraye-kirayen da sojoji su hambarar da gwamnatin, wadda tsarin dimukuradiyya ne ya kawo ta.
Shugaban sojin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake bude wani taron kara wa juna sani ga sashen sakatarori na hedikwatar sojoji da ake gudanarwa a Abuja.
Don haka ya bukaci hafsoshi da sojojin Nijeriya da su kasance masu kwarewa da jajircewa da kuma yin aiki bisa tsarin mulki.
Janar Lagbaja ya nanata cewa sojojin Nijeriya na iya yinsu dan ganin sun kare martabar dimokuradiyya.