Kasar Sin tana son yin aiki tare da kasar Cuba don aiwatar da muhimman matsaya da manyan shugabannin jam’iyyun da kasashen suka cimma, da kuma ci gaba da nuna goyon baya ga juna kan batutuwan da suka shafi muhimman muradun juna, a cewar Li Xi, wani babban jami’in JKS wanda yake kai ziyara kasar Cuba.
Li Xi, mamban zaunannen kwamitin hukumar siyasa na JKS ya bayyan hakan ne a lokacin da yake ganawa da sakataren farko na kwamitin koli ta jam’iyyar kwaminis ta Cuba, kana shugaban kasar Cuba Miguel Diaz-Canel.
Li ya kai ziyarar sada zumunta a Cuba daga ranar Asabar zuwa Litinin.
Li wanda har ila yau shi ne sakataren koli na kwamitin ladabtarwa na JKS ya bayyana cewa, kasar Sin a shirye take ta sa kaimi ga bunkasuwar tsarin jam’iyya da tsarin gurguzu.
Ya kuma kara da cewa, kasar Sin tana son yin aiki tare da kasar Cuba, wajen sa kaimi ga aiwatar da shirin raya kasa da kasa, da shirin tsaro na duniya, da shirin wayewar kai, da gina al’umma mai makoma daya ga bil’adama. (Yahaya)