Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi, ya gana da manyan kusoshin kasashen Afirka da dama da suka zo kasar Sin don bude bikin baje kolin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Afirka karo na hudu, da kuma halartar taron ministoci masu kula da aiwatar da sakamakon taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka (FOCAC) a Changsha, babban birnin lardin Hunan na tsakiyar kasar Sin, a jiya Alhamis.
Yayin ganawarsa da firaministar kasar Uganda, Robinah Nabbanja, Wang ya bayyana cewa, shugabannin kasashen Sin da Uganda sun kulla abota da amincewa da juna, da samar da kuzari da ba da tabbaci domin yaukaka zumuncin da ke tsakanin kasashen biyu. Ya kara da cewa, a cikin rubu’in farko na bana, kayayyakin da Uganda ke fitarwa zuwa kasar Sin sun karu da kusan kashi 90 cikin dari a mizanin shekara-shekara, kuma Sin na son zurfafa hadin gwiwa a aikace a fannoni daban-daban tare da kasar.
- Gwamnatin Tarayya Ta Dukufa Wajen Karya Farashin Kayan Abinci – Minista
- Ƴansanda Sun Cafke Masu Garkuwa Da Mutane 2, Sun Ceto Mutane 11 A Delta Da Katsina
A nata bangaren, Nabbanja ta bayyana godiyarta ga kasar Sin bisa gagarumin goyon bayanta ga gina ababen more rayuwa da bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Uganda na tsawon lokaci. Ta yi nuni da cewa, tana fatan za a zurfafa hadin gwiwa da kasar Sin a muhimman fannoni kamar fadada filin jiragen sama, da yin sauye-sauye na zamani, da kuma zamanantar da aikin gona.
A yayin ganawarsa da mataimakin shugaban kasar Laberiya, Jeremiah Kpan Koung kuwa, Wang ya bayyana cewa, shugabannin Sin da Laberiya sun gana a gefen taron kolin FOCAC na Beijing, inda suka sanar da kulla huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu. Ya ce, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da Laberiya, don ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin shugabannin kasashen biyu, da kuma muhimman sakamakon da aka cimma a taron don samar da moriya ga jama’ar kasashen biyu.
Da yake nasa jawabin, Koung ya nuna godiya da irin goyon baya na tsawon lokaci da kasar Sin take ba Laberiya ba tare da nuna son kai ba, yana mai bayyana aniyar yin aiki tare da kasar Sin wajen aiwatar da matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da zurfafa hadin gwiwa a fannoni daban-daban kamar su harkokin teku, da makamashi mai tsafta, da kiwon lafiya da kuma aikin gona. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp