Wani babban jami’in wata jaridar kasar Aljeriya ya bayyana cewa, shawarar Ziri Daya da Hanya Daya (BRI) da kasar Sin ta gabatar, ta taimaka wajen kare hakkin bil’Adama a cikin kasashen da ke raya shawarar, ganin yadda shawarar ta taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin kasashen da ma ci gaban zamantakewar al’umma.
A yayin wata hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua na baya-bayan nan, darektan yada labarai na jaridar Le Jeune Independent da ake wallafawa a harshen Faransanci, Kamel Mansari ya bayyana cewa, hakkin dan Adam mafi muhimmanci, shi ne ‘yancin rayuwa da samun bunkasuwa. (Ibrahim)