Kasar Sin za ta yi aiki tare da Masar wajen tabbatar da daidaiton da shugabannin kasashen biyu suka cimma da karfafa amincewa da juna ta fannin siyasa, a cewar wani babban jami’in jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin JKS a yayin ziyarar da ya kai Masar.
Li Xi, zaunannen mamban ofishin kula da harkokin siyasa na kwamitin koli na JKS ne ya bayyana hakan yayin ganawa da shugaban kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi.
Li ya kai ziyarar aiki ta sada zumunta a Masar daga ranar Asabar zuwa Litinin.
- ‘Yan Wasan Kasar Sin Sun Lashe Lambar Zinare Ta Farko A Gasar Wasannin Asiya Karo Na 19
- An Gabatar Da Rahoton Bunkasuwar Kamfanoni Mallakar Gwamntin Tsakiyar Sin Na 2023
Li ya kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da ba da goyon baya ga kasar Masar kan batutuwan da suka shafi muhimman muradun juna, inda ya ci gaba da cewa, kasar Sin za ta sa kaimi ga hadin gwiwa tsakanin shawarar shawarar ziri daya da hanya daya da shirin hangen nesa na Masar na shekarar 2030.
Li, wanda kuma shi ne sakataren kwamitin ladabtarwa na JKS, ya bayyana fatan bangarorin biyu za su inganta mu’amala tsakanin jam’iyyun juna da yaki da cin hanci da rashawa.
Sisi a nasa bangare ya yaba da kyakkyawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Masar, ya ce, Masar na son karfafa hadin gwiwa da kasar Sin a fannonin samar da ababen more rayuwa, noma, yawon bude ido, da kudi. Ya bayyana cewa, ana maraba da karin kamfanonin kasar Sin da su zuba jari a Masar. (Yahaya)