Kwanan nan, wani dan jarida na babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG ya yi hira da babban sakataren kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai wato SCO, Nurlan Yermekbayev, a sakatariyar SCO da ke nan birnin Beijing. A cikin hirar, Yermekbayev ya bayyana cewa, kasar Sin a matsayinta na kasar da ke jan ragamar shugabancin SCO tana taka rawar gani sosai.
Yermekbayev ya kara da cewa, kasar Sin a matsayinta na mai shugabancin SCO, ta mai da hankali kan muhimman fannoni takwas na samun ci gaba mai dorewa, wadanda suka hada da rage talauci, da bunkasa tattalin arziki na fasahar zamani, da raya masana’antu, da raya sana’o’i marasa gurbata muhalli, da kiwon lafiyar jama’a, da samar da abinci, kana ta karbi bakuncin wasu ayyuka na musamman a jere.
Da yake magana game da taron kolin kungiyar SCO da za a yi nan ba da dadewa ba a birnin Tianjin na kasar Sin, Yermekbayev ya ce, ana sa ran taron zai zartas da sanarwar Tianjin, wanda zai nuna matsayin kasashe mambobin kungiyar kan batutuwan da suka shafi kasa da kasa, da ci gaba a fannoni daban daban, ciki har da siyasa, da tsaro, da tattalin arziki. Haka kuma za a tsara dabarun ci gaban SCO na shekaru 10 masu zuwa a taron.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp