Ranar 3 ga watan Satumbar shekarar nan ta 2025, babbar rana ce da ta cancanci a tuna da ita, inda kasar Sin ta gudanar da gagarumin bikin faretin soja a Beijing, don tunawa da tarihi, da jarumai da ’yan mazan jiya, da nuna kishin zaman lafiya, tare da kirkiro kyakkyawar makoma.
A gun bikin maraba da baki da suka shigo Beijing don halartar bikin murnar cika shekaru 80 da samun nasarar yakin da al’ummar kasar Sin suka yi da mamayar dakarun Japan da yakin duniya na kin tafarkin murdiya da aka yi ranar 3 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, tarihin ya nuna mana cewa, ba za a iya girgiza imanin dan Adam ga neman adalci ba, kana, ba za a iya kawo cikas ga kyakkyawan fata na wanzar da zaman lafiya ba, har ila yau, ba za a iya samun galaba kan karfin dan Adam ba!
A halin yanzu, kasar Sin tana bin hanyar zamanantar da kai bisa salon kanta, don raya kasa, da farfado da al’umma daga dukkan fannoni, hanyar da ta kasance irinta mai haske da jama’ar kasar ke bi wajen jin dadin rayuwa, kana, hanya mai adalci da dan Adam ke bi wajen shimfida zaman lafiya da samar da ci gaba a duniya. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp