A jiya Jumma’a 5 ga wannan wata, babban taron MDD karo na 79 ya jefa kuri’a tare da zartas da kudurin hadin gwiwar dake tsakanin MDD da kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai wato SCO da kasar Sin da dukkan kasashe membobin kungiyar SCO kimanin 40 suka gabatar tare.
Kudurin ya amince da muhimmiyar rawar da kungiyar SCO ta taka wajen sa kaimi ga samun zaman lafiya da bunkasa da yin imani da juna da kuma hadin gwiwa a yankin, kana ya yaba wa kungiyar SCO bisa kokarin nuna goyon baya ga ayyukan MDD, da kara yin hadin gwiwa a tsakaninta da tsarin MDD.
Mukaddashin shugaban tawagar dindindin ta Sin dake MDD Geng Shuang ya bayyana yayin da yake bayani game da kudurin cewa, a cikin shekaru 24 da kafuwar kungiyar SCO, an samu babban ci gaba bisa tunanin Shanghai, kungiyar ta riga ta kasance kungiya mafi girma ta yanki a duniya. Muhimmin batu a yayin taron kolin Tianjin na kungiyar SCO shi ne yadda shugaba Xi Jinping ya gabatar da shawarar inganta jagorancin duniya wato GGI a gun taron kungiyar SCO plus. Bangarori daban daban sun amince tare da maraba da wannan shawara, bisa tsammanin cewa, ana bukatar tunani da tsarin jagorancin duniya a halin yanzu, don haka shawarar GGI da Sin ta gabatar ta yi matukar dacewa. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp