Jiya Alhamis, babbar darektar asusun ba da lamuni na duniya wato IMF Kristalina Georgieva ta kira wani taron manema labarai kan ajandar manufofin duniya. A cewarta, za a ga farfadowar tattalin arzikin kasar Sin sosai a bana, ganin yadda kasar take ci gaba da bude kofarta da yin kwaskwarima a gida, ana kuma sa ran kasar Sin za ta ba da gudummawar kusan kashi daya bisa uku na ci gaban tattalin arzikin duniya.
Kristalina Georgieva ta kara da cewa, Sin na ba da babban tasiri ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya. Alal misali, idan Sin ta samu karuwar kashi 1% a tattalin arzikinta, to sauran kasashen dake da alaka da ita a fannin tattalin arziki, za su samu karin karuwar kashi 0.3%.
A wani rahoton da asusun na IMF ya fitar a jiya na cewa, farfadowar tattalin arzikin kasar Sin, zai samar da wani sabon kuzari ga tattalin arzikin yankin Asiya, kuma ana sa ran yankin na Asiya zai ba da gudummawar sama da kashi 70% ga ci gaban tattalin arzikin duniya a shekarar 2023 da muke ciki. (Amina Xu)